Jerin lokuta 5 da tsohon mataimakin Shugaban kasa Atiku yayi takarar kujerar shugaban kasa

Jerin lokuta 5 da tsohon mataimakin Shugaban kasa Atiku yayi takarar kujerar shugaban kasa

Yayin da babban zaben shekarar 2023 ke gabatowa, akwai rade -radin cewa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar na iya sake tsayawa takarar shugaban kasa.

Dansa, Adamu Atiku Abubakar, ne ya fara hasashen lokacin da ya bayyana a watan Yuni 2020 cewa Atiku zai sake tsayawa takara.

Duk da cewa da yawa ba su sani ba, burin Atiku na mulkin Najeriya ya fara ne kimanin shekaru 29 da suka gabata!

Jerin lokuta 5 da tsohon mataimakin Shugaban kasa Atiku yayi takarar kujerar shugaban kasa
Tsohon mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar yayi takarar kujerar shugaban kasa sau biyar Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Depositphotos

Zuwa yanzu, ya yi takarar shugabancin Najeriya sau biyar kuma 2023 zai zama na shida idan ya sake tsayawa takara.

1992/93: Takarar shugaban kasa na farko

Kudirin Atiku na takarar shugaban kasa ya fara ne a shekarar 1992 a lokacin jamhuriya ta uku. Ya tsaya takarar fidda gwani na shugaban kasa na jam'iyyar Social Democratic Party (SDP). Amma, ya zo na uku a matakin farko bayan marigayi Cif Moshood Abiola, wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka soke a ranar 12 ga Yuni 1993.

Kara karanta wannan

Rufe iyakokin kasa ya matukar taimaka wa Najeriya, Buhari ga sarauniyar Netherlands

Ku lura, cewa saboda Abiola ya samu kuri'u kusan 400 ne kawai, sai aka shirya zagaye na biyu amma Atiku ya janye masa.

2006/07: takarar shugaban kasa na biyu

A watan Nuwamba na shekarar 2006, Atiku ya sake bayyana cewa zai tsaya takarar shugaban kasa. Daga karshe ya fito a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Action Congress (AC).

Duk da haka, ya sha kaye a zaben, inda ya zo na uku a bayan dan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Umaru Yar'Adua, da dan takarar All Peoples Peoples Party (ANPP), Muhammadu Buhari, wanda yanzu shine shugaban Najeriya, a karkashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

2010/11: Takarar shugaban kasa na uku

Bayan shan kaye a 2007 a jam’iyyar AC, Atiku wanda ya kasance mataimakin shugaban Najeriya a jam’iyyar PDP (1999 zuwa 2007) ya koma jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Jerin sunaye: Manyan 'yan siyasa 5 da aka kayar a 2019 wadanda ka iya dawowa da karfi a shekarar 2023

A watan Oktoban 2010, ya sake bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasar. Sai dai, ya rasa tikitin takarar tsohon shugaban ƙasa a hannun Goodluck Jonathan wanda ya ci nasara a zaɓen.

2014/2015: Takarar shugaban kasa na hudu

Bayan shan kaye a PDP, Atiku ya koma sabuwar jam’iyya, APC, a 2015 don neman kujerar siyasa ta daya a kasar. Abin takaicin shine, ya rasa tikitin takara ga Shugaba Buhari.

2018/2019: Takarar shugaban kasa na biyar

Bayan ya kasa cimma burinsa a APC, Atiku a watan Nuwamba 2017 ya sake komawa PDP. Duk da cewa ya ci zaben fidda gwani na shugaban kasa, Atiku bai iya cika burinsa ba saboda Shugaba Buhari ya sake kayar da shi.

Kungiya ta yi ikirarin cewa Atiku ya shirya sosai don kwace mulki daga APC

A wani labarin, wata kungiya a karkashin inuwar Amalgamated Atiku Support Group ta nuna goyon bayanta ga tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar don ya gaji Shugaba Muhammadu Buhari a 2023.

Kara karanta wannan

Shekaru 39 da bada kwangila, ba a soma aikin samar da lantarki a tashar Mambila ba

Jagoran kungiyar na kasa, Oladimeji Fabiyi, a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, 3 ga watan Satumba, ya ce Atiku shi ne dan siyasa mafi shiri kuma gogaggen dan siyasa da zai kwace mulki daga hannun jam’iyyar APC.

Fabiyi ya kuma yi Allah wadai da sanarwar baya-bayan nan da aka danganta ga wata kungiya da ke ba da shawarar cewa jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) kada ta tsayar da Atiku a matsayin dan takarar shugaban kasa a babban zabe mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel