'Yan Boko sun kai farmaki Babbangida a Yobe, sun yi artabu da sojojin Najeriya

'Yan Boko sun kai farmaki Babbangida a Yobe, sun yi artabu da sojojin Najeriya

  • Mayakan Boko Haram a yanzu haka suna luguden wuta a garin Babbangida da ke karamar hukumar Tarmuwa ta Yobe
  • Majiya daga garin ta tabbatar da cewa yanzu haka ana musayar wuta tsakanin sojojin da suke yankin da miyagun
  • Tuni dai mazauna yankin suka balle tare da tserewa zuwa dajikan da ke kusa domin tsira da ransu da lafiyarsu

Yobe - Miyagun 'yan ta'adda da ake zargin mayakan Boko Haram ne a halin yanzu suna luguden wuta a Babbangida, hedkwatar karamar hukumar Tarmuwa ta jihar Yobe.

Wata majiya ta tabbatar da cewa a halin yanzu ana musayar wuta tsakanin dakarun sojin da ke wurin da 'yan ta'addan, Daily Trust ta wallafa.

Da duminsa: 'Yan Boko na lugugen wuta yanzu haka Babbangida, jihar Yobe
Da duminsa: 'Yan Boko na lugugen wuta yanzu haka Babbangida, jihar Yobe
Source: Original

Daily Trust ta ruwaito cewa, kamar yadda yace, mazauna yankin da yawa sun dinga gudu tare da neman wurin tsira a dajikan yankin.

Read also

'Yan fashin daji sun koma hawa rakuma yayin da dokar siyan fetur a jarkoki ta tsananta

"A halin yanzu muna dajika inda muka tsere domin gujewa mutuwa; Na tabbatar kana iya jin karar harsasai da harbe-harbe," majiyar tace.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Adamu Gidado, wani mazaunin Babangida, wanda ya kubuce zuwa garin Damaturu yayin da aka fara ruwan wutar, ya sanar da Premium Times cewa mazauna yankin sun tsere zuwa daji.

Gidado ya ce ya ga sojoji masu yawa sun dumfari Tarmuwa yayin da yake hanyarsa ta zuwa Damaturu.

"Jama'ar Babangida sun tsere zuwa dajika domin tsoro. Na ga sojoji sun tunkaru garin yayin da na ke juyawa zuwa Damaturu," Gidado yace.
Wata majiyar tsaro ta tabbatar da cigaban inda tace "'Yan Boko Haram a halin yanzu suna musayar wuta da dakarun soji a Babbangida. Amma mun sake tura wasu sojojin masu yawa," majiyar tace.

Har a halin yanzu babu bayanai sosai game da harin.

Read also

Da duminsa: An hallaka kimanin Sojojin Najeriya 30 a jihar Borno

'Yan bindiga sun kallafa wa manoman jihar Katsina haraji

A wani labari na daban, sakamakon hauhawar ta’addanci a fadin jihar Katsina, manoma da dama sun hakura da noma gonakin su sakamakon yadda ‘yan bindiga suka tilasta musu biyan harajin gonakin su.

Kamar yadda gwamnatin jihar Katsina ta kiyasta, gonaki 5,884 wadanda da ake noma wa aka dena saboda farmakin da ake kaiwa gonakin akai-akai.

Daga watan Janairu zuwa Yunin 2021 kamar yadda gwamnatin jihar ta bayyana, an dakatar da noma hectare 23,333 na gonaki 2,924.

Source: Legit Newspaper

Online view pixel