Da duminsa: An hallaka kimanin Sojojin Najeriya 30 a jihar Borno
- Yan Boko Haram sun kaiwa jami'an Sojin Najeriya harin kwantar bauna
- Sojojin na cikin wadanda suka samu hutu don zuwa gida
- Shugaba Buhari ya bayyanawa majalisar dinkin duniya cewa an nakasa Boko Haram
Borno - Wasu da ake zargin yan ta'addan Boko Haram/ISWAP sun budewa jami'an Sojojin Najeriya wuta ranar Juma'a yayinda suke hanyarsu ta zuwa Maiduguri daga Marte.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa wannan hari ya auku ne tsakanin Dikwa da Marte, inda yan ta'addan suka rika harbawa Sojoji roka.
Marte na da nisan Kilomita 180 daga Maiduguri kuma yana daya daga cikin kananan hukumomin Bornon da mutane sun arce daga muhallansu zuwa Monguno da Maiduguri.
Wata majiya tace:
"Abinda ya faru da Sojoji a hanyar Marte-Dikwa abin tada hankali ne kuma gargadi kan cewa har yanzu da sauran rina a kaba."
Sojojin da aka baiwa hutun zuwa wajen iyalansu aka kaiwa hari
Majiyar ta kara da cewa wadannan Sojoji da aka kashe sun samu hutu ne bayan kwashe dogon lokaci a faggen daga domin ganin iyalansu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Majiyar tace:
"Yayinda Sojoji ke hanyarsu ta zuwa Maidugri daga Marte, yan ta'addan ISWAP suka bude wuta motocin da ke dauke da su, inda aka hallaka kimanin 30 cikinsu kuma har yanzu ba'a san inda wasu suke ba."
Da farko wata majiya ta bayyanawa Vanguard cewa sojoji 16 ne suka rasa rayurwasu a yayin harin, amma a ranar Asabar da yamma labari yazo cewa Soji 30 aka kashe yayinda wasu suka samu raunika daga harbin bindiga.
Duk wani yunkurin ji ta bakin kaakin Sojin yaci tura, sannan hukumar bata saki wani jawabi akan lamarin ba har yanzu.
Yan Boko Haram sun fara horar da yan bindiga a Kaduna, Majiyoyi
Wasu gungun yan Boko Haram sun garzaya Kaduna daga Arewa maso gabas domin fara horar da yan bindiga masu garkuwa da mutane a Arewa maso yammacin Najeriya.
Majiyoyi biyu daga gidan Soja sun bayyanawa Agence France Presse (AFP) ranar Juma'a yan Boko Haramun na horar da yan bindiga wajen amfani da makamai.
Wannan alamu ne dake nuna cewa an fara shirin hadin kai tsakanin yan Boko Haram da yan bindiga.
Asali: Legit.ng