'Yan fashin daji sun koma hawa rakuma yayin da dokar siyan fetur a jarkoki ta tsananta

'Yan fashin daji sun koma hawa rakuma yayin da dokar siyan fetur a jarkoki ta tsananta

  • Mazauna yankunan Sokoto sun tabbatar da cewa 'yan bindiga yanzu sun koma amfani da rakuma saboda rashin fetur
  • Har ila yau, mazauna yankin sun ce Turji, shugaban 'yan bindiga ya na gayyato mutanensu inda suke shirya daba a dajikan Sokoto
  • Sarkin Gobir Isa, ya rantse da Qur'ani kan cewa ba shi da hannu a farmakin da ake kai wa jama'arsa kamar yadda aka zargesa

Sokoto - 'Yan fashin dajin da tsananin dokar hana siyan fetur a jarkoki ta dama a halin yanzu sun koma amfani da rakuma, kamar yadda majiyoyi suka sanar.

A cikin makon da ya gabata ne 'yan sanda suka dinga cafke jama'a da aka gano suna kai wa 'yan fashin dajin fetur a cikin dajika, Daily Trust ta ruwaito.

'Yan fashin daji sun koma hawa rakuma yayin da dokar siyan fetur a jarkoki ta tsananta
'Yan fashin daji sun koma hawa rakuma yayin da dokar siyan fetur a jarkoki ta tsananta. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

A kalla gwamnoni uku na yankin arewa maso yamma ne suka haramta siyar wa masu jarkoki man fetur domin dakile farmakin 'yan bindiga.

Kara karanta wannan

Datse sadarwa: 'Yan bindiga na amfani da layikan Nijar wurin kai farmaki, Dan majalisa

Wani mazaunin Sokoto, wanda ya bukaci a boye sunansa, ya sanar da Daily Trust cewa 'yan bindigan da ke tserewa daga jihar Zamfara zuwa Sokoto na cigaba da hada kungiyoyinsu a Sokoto sakamakon gayyatar da fitaccen gagararren shugaban 'yan bindiga mai suna Turji ya aike musu da shi.

Ya ce a kalla yanzu akwai sama da kungiyoyi 20 na 'yan fashin dajin a yankin kuma duk sun iso ne rakuma saboda basu da fetur a baburansu.

Majiyar ta kara da cewa 'yan bindiga suna amfani da rakuma wurin kai farmaki yankunansu tare da garkuwa da jama'a.

Kwamishinan tsaro na jihar, Kanal Garba Moyi mai ritaya, ya ce babu wani shaidar cewa 'yan bindigan na sake hada kungiyoyinsu a yankin.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, hakimin Isa, Alhaji Nasiru Ahmad, ya yi rantsuwa da Qur'anic kan cewa baya bai wa 'yan bindigan taimako a jihar.

Kara karanta wannan

Babban magana: Boko Haram sun fara koya wa 'yan bindiga yadda ake harbo jirgin sojoji

A makon da ya gabata ne wasu fusatattun jama'a suka kai farmaki fadarsa tare da kai wa wasu jama'ar Moyi hari sakamakon zargin basaraken da suka yi da bai wa 'yan bindigan garkuwa.

An tattaro cewa, basaraken ya tashi tsaye a masallacin Juma'a jim kadan bayan kammala sallar kuma ya rantse da cewa baya taimakawa 'yan bindigan.

"Idan har na taba bada gudumawa kan wani farmaki da aka kai wa yankina ko kuma sanar da 'yan bindiga kan wani kaiwa da kawowa na sojoji ko wasu mabiya na, kada Allah ya bani ikon kaiwa wani makon," yace.

A wani bidiyon basaraken wanda ya karade kafafe sada zumuntar, Sarkin Gobir Isa, ya ce ya fi kowa a yankin shiga takaici da bakin ciki idan an kai musu farmaki.

Sojin Najeriya sun dakile farmakin da ISWAP suka kai sansanin soji da wasu yankunan Yobe

A wani labari na daban, a yammacin ranar Alhamis ne dakarun sojin Najeriya su ka yi nasarar dakile wani farmaki da 'yan ta'addan Islamic State of West Africa Province (ISWAP) suka kai sansanin soji da kuma wasu yankuna na jihohin Borno da Yobe.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Hari Shinkafi Bayan Tura Wasiƙa, Sun Kutsa Ofisoshin 'Yan Sanda Sun Saci Bindigu

PRNigeria ta gano cewa, dakarun dauke da manyan makamai sun bankado yunkurin harin da miyagun 'yan ta'addan suka kai Malam Fatori da ke jihar Borno.

'Yan ta'addan da suka bayyana a motocin yaki da babura, zakakuran dakarun sun fi karfinsu inda suka batar da wasu daga ciki yayin da wasu suka ja da baya tare da tserewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng