Adam A. Zango min kishi ne na ki yarda in aureshi, Ummi Rahab

Adam A. Zango min kishi ne na ki yarda in aureshi, Ummi Rahab

  • Jaruma Ummi Rahab ta bayyana abinda ke tsakaninta da Mawaki Adam A Zango
  • Yar wasar Kannywood din ya bayyana cewa Zango na matsayin Uba ne a wajenta
  • Ta yi bayanin yadda aka cireta daga wani Fim ba tsamanni

'Yar wasar kwaikwayo na masana'antar Kannywood, Ummi Rahab, ta yi magana kan dambarwar da ke tsakaninta da dan wasa kuma mawaki, Adam A. Zango.

A hirar da tayi da DailyTrust, Ummi Rahab ta bayyana cewa Adam A Zange ya cire ta daga wasu fina-funai da ya kamata ace ta fito.

Amma a ra'ayinta, wannan ba komai bane saboda a matsayinsa na ubangidanta, yana da ikon cireta daga Fim.

Yayinda aka tambayeta kan lamarin cire a Fim tace:

"Gaskiya haka ne, amma wannan ba komai ba ne, tunda yana da iko ya saka ko ya cire wanda ya ga dama a fim dinsa.

Kara karanta wannan

Daga 1 ga watan Oktoba matsalolin Najeriya za su kau, inji hasashen wani Fasto

"Babu shakka ina daga cikin wadanda aka shirya za su fito a cikin fim dinsa ‘Farin Wata Sha Kallo’ da ake nunawa a YouTube, amma ban san dalili ba sai suka cire ni."

Kishi ke damunsa

Ummi Rahab ta kara da cewa Adam Zango na kishi ne kawai saboda tana soyayya da wani sabaninsa duk da yayi kokarin hanata.

A cewarta, Adam Zango na matsayin Uba ne gareta amma da alamun bai fahimci hakan ba.

Tace:
"Na fada wa wadansu aminaina cewa Adam Zango yana kishi ne saboda na fara soyayya da wadansu samari, ya yi kokarin ya hana ni, amma na nuna masa cewa shi fa uba ne.
Da ya ga ba zan yarda da ra’ayinsa ba shi ne ya fara bore."

Asali: Legit.ng

Online view pixel