'Yan mata gareku: Fitaccen Malamin, Zakir Naik yana nema wa ɗan shi matar aure

'Yan mata gareku: Fitaccen Malamin, Zakir Naik yana nema wa ɗan shi matar aure

  • Fitaccen malamin addinin musulunci da ke kasar Indiya, Zakir Naik ya na nema wa dan sa Fariq matar aure
  • A cewar sa, matar ta kasance musulma mai dabi’u masu kyau, mai digiri a fannin musulunci da sauran suffofi
  • Ta kasance wacce za ta karfafa wa dan sa guiwa wurin da'awah kuma za ta iya komawa kasar Malaysia da zama

Malaysia - Fitaccen malamin addinin musulunci, Zakir Naik ya yi wata wallafa a shafin sa na Facebook inda ya ke nema wa dan sa Fariq Zakir Naik matar aure.

A cewar sa, ya na nema wa dan sa Fariq mata musulma mai tarbiyya mai kyau yadda za su kasance fitilu masu haska wa juna rayuwa.

'Yan mata gareku: Fitaccen Malamin, Zakir Naik yana nema wa ɗan shi matar aure
'Yan mata gareku: Fitaccen Malamin, Zakir Naik yana nema wa ɗan shi matar aure. Hoto daga Muryarhausa.com
Asali: UGC

A wallafar wacce yayi ta shafin sa na Facebook, ya ce mahaifi ko waliyyin matar ya yi masa magana da kuma bayanan da ake bukata.

Kara karanta wannan

Daga 1 ga watan Oktoba matsalolin Najeriya za su kau, inji hasashen wani Fasto

Kamar yadda ya wallafa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ina nema wa da na Fariq matar aure, musulma ta kwarai mai dabi’u masu kyau yadda da na da matar sa za su kasance haske ga juna.
"Idan kai mahaifi ko kuma dan uwa wanda ya amince da wannan ne, ya yi gaggawar kawo bayanai."

Malamin addinin ya bayyana abubuwa da halayen da ake bukatar matar dan sa ta mallaka

Kamar yadda ya yi wallafar wacce ta samu tsokaci fiye da 1,900, cikin halayen da ya ke bukata ya ce matar ta kasance musulma ta kwarai wacce ba ta aikata haram.

Hakazalika, ba ta ta’allakar da rayuwar ta wurin wadaka da shagulgulan duniya ba, ta kasance ta na da digiri a wanni fanni na musulunci, ta iya turanci kwarai, za ta iya zama a Malaysia da sauran su.

Naik ya wallafa wasu daga cikin abubuwan da dan sa ya mallaka da kuma bayanai a kan mahaifiyar Fariq da shi kan sa mahaifin da ‘yan uwan sa.

Kara karanta wannan

Rundunar soji: Muna mutunta su ne kawai, ba tarairayar tubabbun 'yan ta'adda mu ke ba

Da yawa daga cikin masu sukar Buhari su kan lallaɓa Villa diɓar 'jar miya'

A wani labari na daban, Femi Adesina, mai bada shawara na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari kan yada labarai, ya ce wasu daga cikin manyan masu caccakar shugaban kasan a fili suna lallabawa Aso Rock domin cin abincin dare da shi.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, mai magana da yawun shugaban kasan ya sanar da hakan ne yayin tsokaci kan komen da Femi Fani-Kayode yayi zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

A makon da ya gabata bayan shugaban kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC na kasa kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya gabatar da shi a gaban Buhari a gidan gwamnatin tarayya da ke Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel