Rundunar soji: Muna mutunta su ne kawai, ba tarairayar tubabbun 'yan ta'adda mu ke ba
- Kwamandan rundunar hadin guiwa da ke yankin arewa maso gabas ya musanta cewa suna tarairayar 'yan ta'adda
- Ya ce suna mu'amala da tubabbun 'yan ta'addan ne kamar yadda za a yi wa kowanne dan Adam ba dabba ba
- Ya kara da cewa, hatta a filin yaki idan makiyi ya ce ya tuba, baka da hurumin cigaba da yakarsa, sai dai zaman sasanci
Borno - Christopher Musa kwamandan rundunar hadin guiwa ta arewa maso gabas, operation Hadin Kai, ya ce rundunar soja ba ta tarairaya da yi wa tubabbun 'yan ta'adda gata, TheCable ta ruwaito.
A yayin jawabi a wata tattaunawa da manema labarai a ranar Laraba, Musa ya ce hukuncin barin 'yan ta'adda su mika wuya ga sojoji lamari ne da yayi daidai da dokokin kasashen duniya.
Ya ce idan makiyi ya mika wuya yayin yaki, ba a amince sojoji ko mayakan su harbi wannan makiyin ba. Ya ce dole ne rundunar ta dinga mu'amala da su kamar yadda za ta yi da mutane.
"Ban sani ba ko jama'a ba su fahimce mu ba ne, shiyasa suke ganin kamar muna tarairayarsu. In har mutum ba shi da lafiya, ya dace a bashi magani, idan ya na jin yunwa, a bashi abinci, a bashi gida kamar kowa. Kuma hakan mu ke musu," Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito yadda yace.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Don haka babu batun tarairaya. Muna mutunta su ne tamkar kowanne dan Adam.
"Hakazalika, ina son sanar da jama'a cewa babu wani batun tarairaya. Muna tantance su ne domin gano wadanda ba su taba kai farmaki ba da wadanda suka saba yaki."
Kwamandan ya kara da shawartar sauran 'yan ta'addan da basu mika wuya tare da yada makamai da su yi hakan tun kafin lokaci ya kure musu, TheCable ta wallafa.
Fusatattun 'yan fansho sun garkame SSG na Ogun kan rike N68bn na garatutinsu
A wani labari na daban, fusatattun 'yan fansho na jihar Ogun a ranar Laraba sun rufe sakateriyar jihar inda ofishin gwamnan ya ke da zanga-zanga saboda kin biyansu kudinsu har N68 biliyan kusan shekaru goma kenan da suke bin gwamnatin.
Daily Trust ta ruwaito cewa, 'yan fanshon da ke karkashin kungiyar karamar hukuma sun mamaye manyan kofofi 2 na sakateriyar da ke Oke-Mosan a Abeokuta inda suka hana SSG Tokunbo Talabi da sauran ma'aikatan shiga tsawon sa'o'i hudu.
Masu zanga-zangar sun tafi dauke da takardu wadadna aka yi rubuce-rubuce daban-daban domin nuna fushinsu kan lamarin.
Asali: Legit.ng