Da yawa daga cikin masu sukar Buhari su kan lallaɓa Villa diɓar 'jar miya'

Da yawa daga cikin masu sukar Buhari su kan lallaɓa Villa diɓar 'jar miya'

  • Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya ce wasu masu caccakar Buhari fuska biyu gare su
  • Ya bayyana yadda suke sukar Buhari a fili da gidajen talabijin amma suke lallabawa wurinsa cin abincin dare
  • Ya tuna yadda FFK ke zagin Buhari, iyalansa da jam'iyya mai mulki amma Buhari ya karbe shi bayan ya dawo

Femi Adesina, mai bada shawara na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari kan yada labarai, ya ce wasu daga cikin manyan masu caccakar shugaban kasan a fili suna lallabawa Aso Rock domin cin abincin dare da shi.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, mai magana da yawun shugaban kasan ya sanar da hakan ne yayin tsokaci kan komen da Femi Fani-Kayode yayi zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Kara karanta wannan

Duk da yi wa Yusuf Buhari fatan mutuwa, shugaba Buhari ya yafewa Fani-Kayode

Daga cikin masu sukar Buhari akwai masu zuwa cin abincin dare wurin shi, Femi Adesina
Daga cikin masu sukar Buhari akwai masu zuwa cin abincin dare wurin shi, Femi Adesina. Hoto ddaga dailytrust.com
Asali: UGC

A makon da ya gabata bayan shugaban kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC na kasa kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya gabatar da shi a gaban Buhari a gidan gwamnatin tarayya da ke Abuja.

Daga 'yan jam'iyyar APC mai mulki har da na jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party sun dinga caccakarsa kan sauya shekar nan, Daily Trust ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A rubutun Adesina na mako-mako, ya ce Buhari ya na da zuciya mai kyau kuma yadda ya karba Fani-Kayode ya bayyana hakan.

"Tsakanin makon da ya gabata zuwa yanzu, ana ta caccakar mu kan komowar FFK. Ya ce abubuwa marasa dadin ji wanda mutum ba zai iya yafe masa ba."
“Ya caccaki shugaban kasa, iyalansa, ya yi wa Yusuf Buhari fatan mutuwa lokacin da yayi hatsari, abubuwa daban-daban.

Kara karanta wannan

Obasanjo ga Buhari: Ta'addanci ne a yi ta karbo bashi ana barin na baya da biya

“Har cewa yayi gara ya sheka lahira da dai ya koma jam'iyya mai mulki, toh sai ga shi a makon da ya gabata ya dawo da ran shi da lafiyarsa."

Mai magana da yawun shugaban kasan ya ce baya da Fani-Kayode, Buhari ya karba bakunci tare da cin abinci dare da wasu da ke caccakarsa a cikin jama'a.

Ya ce yayin da wasu jama'a suka dauka dabi'ar karya ga Buhari kan cewa ba shi da yafiya, shugaban kasan ya nuna ba haka yake ba.

Rufe iyakokin kasa ya matukar taimaka wa Najeriya, Buhari ga sarauniyar Netherlands

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce rufe iyakokin Najeriya na sama da shekara daya ya matukar taimaka wa Najeriya, TheCable ta ruwaito.

A watan Augustan 2019 ne gwamnatin tarayya ta bada umarnin rufe dukkan iyakokin tudun kasar nan kan shigo da miyagun kwayoyi, makamai da kuma abinci daga kasashen da ke da makwabtaka da Najeriya.

Kara karanta wannan

Dalilin da yasa mambobin APC ke jin haushin shigowar Kayode jam'iyyarsu, DG PGF

A watan Disamban 2020, Buhari ya bada umarnin bude iyakokin tudu hudu na kasar nan. Bayan watanni kadan da bude su, shugaban kasan ya bayyana damuwarsa kan cewa rufe iyakokin tudun bai tsinana komai ba wurin hana shigo da makamai kasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel