Yadda ni da Sanusi II muka rike darajar Naira na tsawon shekara 5 a CBN inji Farfesa Moghalu
- Farfesa Kingsley Moghalu ya bayyana abin da ya jawo Dalar Amurka ta tashi
- Masanin tattalin arzikin ya fadi yadda CBN ta rike darajar Naira a lokacinsu
- A halin yanzu Dala tayi tashin da ba a taba gani ba, ana saida N1 a kan N570
Nigeria - Farfesa Kingsley Moghalu ya yi bayanin yadda bankin CBN ya rike darajar Dala a lokacinsu na tsawon shekaru biyar tsakanin 2009 da 2014.
Tsohon mataimakin gwamnan na CBN ya yi wannan bayani ne a lokacin da Punch ta yi hira da shi ta kafar yanar gizo a ranar 23 ga watan Satumba, 2021.
Kingsley Moghalu ya rike kujerar mataimakin gwamnan bankin CBN a karkashin Sanusi Lamido Sanusi.
A wancan lokaci an rika canzar $1 a kan N150, amma yanzu Dalar ta tashi zuwa N570 a karkashin jagorancin gwamnan babban bankin kasa, Godwin Emefiele.
Da yake magana da ‘yan jarida, Kingsley Moghalu yace Naira tana yin kasa a kasuwar canji ne saboda rashin kafu war CBN a kasa da kuma aikin ‘yan canji.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Menene sirrin Moghalu da Sanusi a CBN?
Farfesa Kingsley Moghalu yace sun iya hana Dala tashi a kan Naira a lokacinsu saboda sun yi kokari sosai wajen jawo kamfanonin da ke zuba hannun jari.
“Mun yi kokari sosai a kan batun farashin kudin kasashen waje. Muna so mu samar da damar da za a zo daga ketare, a zuba hannun jari a tattalin Najeriya.”
“Saboda haka mun san hanyar da za ayi wannan shi ne a samar da tsayayyen farashin kudin waje.”
“Mun tabbatar cewa za ka iya shigo wa da kudinka Najeriya domin kayi kasuwanci, kuma ka maida su 100% na yadda ka zo da su, duk suna nan a na ka.”
Moghalu yace idan Daloli suna shigo wa tattalin arzikin Najeriya, farashin Dalar zai sauka zuwa kusan N400 a kasuwar canji, akasin N570 da ake canji a yau.
A baya kun ji Dalar Amurka tana ta tashi a kasuwar canji duk da babban bankin Najeriya ya dakatar da aikin Aboki Fx da nufin a rage karyewar Naira.
Manema labarai sun ziyarci kasuwar bureau de change na ‘yan canji da ke unguwar Wuse a Abuja, inda suka ga cewa ana saida kowace Dala a Naira 574.
Asali: Legit.ng