An kama ma’aurata kan kashe dansu tare da binne shi cikin sirri saboda ‘rashin ji’

An kama ma’aurata kan kashe dansu tare da binne shi cikin sirri saboda ‘rashin ji’

  • Wasu ma'aurata biyu a jihar Imo sun shiga hannun 'yan sanda bisa zargin halaka dan cikinsu
  • Ma'auratan sun kashe dan nasu tare da binne shi a boye saboda baya jin magana kuma kullun cikin daga masu hankali yake
  • Kakakin 'yan sandan jihar, CSP Michael Abattam a ranar Juma’a ya tabbatar da faruwar lamarin

Imo - Rundunar ‘yan sandan jihar Imo ta cafke wasu ma’aurata bisa zargin kashe dan su mai shekaru 28 tare da binne shi a boye saboda rashin jin magana.

Ma'auratan, Lambert Ukachukwu, matarsa da 'yarsa, wadanda suka fito daga Duruegwele a karamar hukumar Isiala Mbano ta jihar Imo, suna hannun 'yan sanda bisa zarginsu da hada baki don kashe dan su na karshe da aka bayyana da suna Chukwuebuka.

An kama ma’aurata kan kashe dansu tare da binne shi cikin sirri saboda ‘rashin ji’
An kama ma’aurata kan kashe dansu tare da binne shi cikin sirri saboda ‘rashin ji’ Hoto: Premium Times
Asali: UGC

An ce an kashe yaron mai shekaru 28 a ranar Asabar, 7 ga Satumba, 2021, saboda taurin kai da hana danginsa kwanciyar hankali.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi ram da gurgu mai shekaru 22 kan zargin garkuwa da mutane

An samu labarin cewa an bugi marigayi Chukwuebuka da abu mai kaifi a kai sannan aka bar shi yayi ta zubar jini har ya mutu sannan aka binne shi a kusa da gidan iyayensa.

Jaridar The Nation ta samu labarin cewa matasan yankin ne suka cafke dukkanin mutanen da ake zargin bayan sun fara shakku kan inda marigayin ya shiga.

"Lokacin da muka fuskanci mahaifin ya gaya mana cewa yaron ya yi tafiya zuwa Ghana amma lokacin da muka kara matsa masa da barazanar kona gidan, sai 'yar ta tona abun da suka aikata," in ji daya daga cikin matasan.

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, CSP Michael Abattam a ranar Juma’a ya tabbatar da faruwar lamarin ga wakilin jaridar a Owerri.

Kara karanta wannan

EFCC ta kama 'yan damfara ta intanet 30 a jami'ar KWASU

Ya ce:

“Ee gaskiya ne. Zan aiko muku da bayanan gaba daya.”

'Yan sanda sun kama tsohon ɗan majalisa da mutane 2 bisa zargin harkar ƙungiyar asiri

A wani labari na daban, rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta samu nasarar kama wani tsohon dan majalisar jihar, Mr Joseph Adegbesan da wasu mutane 2 da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne.

Kamar yadda Premium Times ta ruwaito, hakan ya biyo bayan korafin su da Oludare Kadiri, dan majalisa mai wakiltar mazabar Ijebu ta arewa II ya kai wa rundunar.

Ana zargin su da shiga hakkin al’umma, kai farmaki ga rayuwar jama’a da mallakar miyagun makamai ba bisa ka’ida ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel