ADC ta yi wa manyan Arewa kaca-kaca saboda kalamansu kan yiwuwar cigaba da rike mulki

ADC ta yi wa manyan Arewa kaca-kaca saboda kalamansu kan yiwuwar cigaba da rike mulki

  • Jam’iyyar African Democratic Congress ta maida wa kungiyar NEF martani
  • Shugaban jam’iyyar adawar, Ralphs Okey Nwosu ya fitar da jawabi a Abuja
  • Ralphs Okey Nwosu ya yi Allah-wadai da kalaman Dr. Hakeem Baba Ahmed

FCT, Abuja - Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta yi tir da kalaman da suka fito daga bakin Dr. Hakeem Baba-Ahmed a kan batun zaben 2023.

ADC ta yi raddi ne bayan darektan yada labarai da wayar da kai na kungiyar NEF, Baba-Ahmed, yace Arewa tana da kuri’un da za ta iya cigaba da mulki.

Daily Trust ta kawo rahoto a ranar Alhamis, 23 ga watan Satumba, 2021, cewa jam’iyyar tana ganin kalaman dattijon za su iya jefa kasar cikin hatsaniya.

Kara karanta wannan

Karya ake yi, ba mu ce mun yi nadamar zaben Buhari a 2015 ba inji Kungiyar Dattawan Arewa

Shugaban jam’iyyar ADC, Ralphs Okey Nwosu ya yi magana ranar Laraba a Abuja, ya zargi kakakin NEC da raba kan jama’a, ganganci da tsokanan fada.

Cif Ralphs Okey Nwosu yace adalci shi ne a bar kowace kabila ta samu damar yin shugabanci, a cewarsa akasin hakan yana iya kai ga kawo rigima a kasa.

Shugaban kasa
Shugaban kasa Buhari a ofis Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahoton yace Ralphs Nwosu ya yi kira ga dattawan kasar su dage ne wajen hada-kan al’umma.

“Rai na yana baci a duk lokacin da wani daga cikin sanannun masanan da ake ganin girmansu ya yi irin wannan maganar.”

A cewarsa bai kamata a maida batun kasar nan ya zama kan yankin Arewa ko bangaren kudu ba.

Ina amfanin badi ba rai?

“Wasu bangare su cigaba da rike mulki sannan a rika samun irin wannan talauci, rashin zaman lafiya da rabuwar kai ba zai ceci kowa ba.”

Kara karanta wannan

Yadda za a fito da Magajin Shugaba Buhari, mun koyi hankali yanzu inji Dattawan Arewa

A madadin jam’iyyar hamayyar, Ralphs Okey Nwosu yace ya zama dole manya su zama masu hada-kai domin a kafa kasar da za ta taimaki kowa da kowa.

Babu cizon yatsa saboda Buhari

Ana ta rade-radin cewa NEF ta na nadamar zaben APC a 2015, amma an ji kakakin kungiyar NEF, Hakeem Baba-Ahmed ya zargi wasu da jirkita maganganunsa.

NEF tayi magana a kan gwamnatin APC, tace babu inda ta ce tayi da-na-sanin mara wa Muhammadu Buhari baya a maimakon Goodluck Jonathan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel