Babu fashi, za mu yi gangami a hedkwatar UN, Masu son kafa kasar Yarabawa

Babu fashi, za mu yi gangami a hedkwatar UN, Masu son kafa kasar Yarabawa

  • Masu gangami karkashin inuwa wata kungiya, NINAS, sun ce babu gudu babu ja da baya, za su yi gangami a ranar Juma'a a UN
  • Gangamin nasu zai yi daidai ne da ranar da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi jawabi a taro na 76 na majalisar dinkin duniya
  • Kungiyar ta zargi gwamnatin Najeriya da bai wa wasu bakaken Amurkawa kudi har $500 domin su fito nuna kaunar Buhari

New York - Masu zanga-zanga tare da gangami karkashin inuwar kungiyar Nigerian Indigenous Nationalities Alliance for Self-Determination (NINAS), sun sha alwashin yin gagarumar zanga-zanga ta 'yanci a hedkwatar majalisar dinkin duniya da ke New York a Amurka, ranar Juma'a.

Gagarumin gangamin da za su yi ya yi daidai da ranar da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi jawabi a taron karo na 76 na majalisar dinkin duniya a ranar Juma'a, The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Yan Taliban sun nemi a basu damar gabatar da jawabi a taron da Buhari ya je a Amurka

Babu fashi, za mu yi gangami a hedkwatar UN, Masu son kafa kasar Yarabawa
Babu fashi, za mu yi gangami a hedkwatar UN, Masu son kafa kasar Yarabawa. Hoto daga thenationonlineng.net
Asali: UGC

Akintoye a wata takarda ta ranar Alhamis da aka bai wa manema labarai, ya zargi gwamnatin tarayya da daukar nauyin wani zanga-zanga a hedkwatar majalisar dinkin duniya mai akasin hakan.

Ya zargi gwamnatin Najeriya da fara hayar bakaken fata da ke zama a Amurka inda aka biya kowanne mutum daya $500 domin zanga-zangar nuna goyon bayan Buhari da kuma fatan hadin kan Najeriya a hedkwatar majalisar dinkin duniya.

Akintoye ya sha alwashin cewa dole ne a fifita bukatar jama'a kuma sai sun fita zanga-zangar NINAS, The Nation ta ruwaito.

Baya ga Akintoye, sakatare janar Tony Nnadi, wanda ya wakilci kungiyar sashin Niger da Farfesa Yusuf Turaki, wanda ya wakilci tsakiyar kasa nan a NINAS, sun hada kai tare da kira ga majalisar dinkin duniya da ta bada taimako wurin hana Najeriya fadawa rudu.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari za ta san matsayar bashin $4bn nan da kwana 7, kwamiti zai zauna

FG ta sanar da dalilin da yasa ba za ta bayyana sunayen masu daukar nauyin ta'addanci ba

A wani labari na daban, Abubakar Malami, antoni janar na tarayya, ya ce gwamnati ba za ta iya bayyana suna tare da tozarta wadanda ta ke zargi da daukar nauyin ta'addanci ba kafin ta gurfanar da su kuma a yanke musu hukunci.

TheCable ta ruwaito cewa, a wata takarda da Umar Gwandu ya fitar, AGF ya ce daga baya za a bayyana wadanda ake zargin bayan an yanke musu hukunci.

"Bayyana sunayensu tare da tozarta su ba ya daga cikin dokokin gwamnatin tarayya kuma ba a mutunta hakkin dan Adam ba da ke bayyana gaskiyarsa har sai an kama shi da laifi," takardar ta ce."

Asali: Legit.ng

Online view pixel