Gwamnatin Buhari za ta san matsayar bashin $4bn nan da kwana 7, kwamiti zai zauna
- Majalisar Dattawa ta ba kwamiti kwanaki 7 ya duba rokon karbo bashin $4bn
- Shugaban majalisa, Ahmad Lawan ya ba kwamitin bashi wannan aikin a jiya
- Sanata Clifford Ordia zai gabatar da rahoto a gaban majalisa a mako mai zuwa
Abuja - Majalisar dattawan Najeriya ta bukaci kwamitin harkar bashi da aron kudi ya fara aiki a kan rokon da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kawo.
Gwamnatin Muhammadu Buhari tana nema majalisar tarayya ta ba ta damar karbo aron dala biliyan $4.054 da kuma €710m da $125m daga kasashen waje.
Daily Trust tace majalisar dattawan ta dauki wannan matsaya ne a ranar Talata, kusan mako guda da karanto wasikar shugaban kasar a zauren majalisar.
Shugaban kwamitin, Sanata Clifford Ordia mai wakiltar yankin jihar Edo ta tsakiya a karkashin jam’iyyar PDP zai zauna a kan batun karbar bashin tiriliyoyin.
Jerin sunaye: Manyan 'yan siyasa 5 da aka kayar a 2019 wadanda ka iya dawowa da karfi a shekarar 2023
Da aka dawo zama a ranar 21 ga watan Satumba, 2021, shugaban majalisar dattawan kasar ya bukaci kwamitin da ke kula da harkar cin bashin ya shiga aiki.
Ahmad Lawan ya ba Clifford Ordia kwanaki bakwai su kammala aikinsu, sai su gabatar da rahotonsu. Kwamitin zai karkare aiki a ranar Talata mai zuwa.
Jaridar Vanguard tace Sanata Yahaya Abdullahi ya tado maganar, inda shugaban marasa rinjaye, Sanata Enyinnaya Abaribe ya yi na’am da a fara aiki kan batun.
Me za a yi da wannan kudi?
Idan an yi nasarar samun wannan bashi ne gwamnatin tarayya za ta aiwatar da ayyukan more rayuwa da ke karkashin tsarin cin bashi na shekara 2018-2021.
Za a karbo aron kudin ne daga wurare irinsu; World Bank, French Development Agency, China Exim Bank, da International Fund for Agricultural Development.
Hala zalika Credit Suisse Group and Standard Chartered/China Export and Credit (SINOSURE) na kasar Sin zai taimaka wajen ba gwamnatin kasar wannan bashi.
An kai kudirin garkuwa da mutane a Majalisa
A ranar Talatar ne aka ji cewa Sanatan jihar Ogun, Ibikunle Amosun yana so duk wanda ya ci kudin da aka samu daa satar mutane ya yi shekaru 30 a kurkuku.
Sanata Ibikunle Amosun ya kawo kudirin da zai yi maganin satar mutane. Muddin kudirin ya zama doka, duk wanda aka kama zai zauna a kurkuku har mutuwa
Asali: Legit.ng