FG ta sanar da dalilin da yasa ba za ta bayyana sunayen masu daukar nauyin ta'addanci ba

FG ta sanar da dalilin da yasa ba za ta bayyana sunayen masu daukar nauyin ta'addanci ba

  • AGF Abubakar Malami ya bayyana cewa gwamnati ba ta da ikon bayyana suna da tozarta wadanda ake zargi da daukar nauyin ta'addanci
  • Ya ce tabbas lokaci zai zo da 'yan Najeriya za su san masu mugun aikin, amma sai an gurfanar da wadanda ake zargi kuma kotu ta yanke hukunci
  • Babban lauyan ya sanar da cewa, a tsarin shari'a da doka ta kasa, mutum ba shi da laifi ko ana zarginsa, har sai kotu ta tabbatar da laifinsa

Abuja - Abubakar Malami, antoni janar na tarayya, ya ce gwamnati ba za ta iya bayyana suna tare da tozarta wadanda ta ke zargi da daukar nauyin ta'addanci ba kafin ta gurfanar da su kuma a yanke musu hukunci.

TheCable ta ruwaito cewa, a wata takarda da Umar Gwandu ya fitar, AGF ya ce daga baya za a bayyana wadanda ake zargin bayan an yanke musu hukunci.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta ce ba ta da sha'awar kunyata masu daukar nauyin ta'addanci

FG ta sanar da dalilin da yasa ba za ta bayyana sunayen masu daukar nauyin ta'addanci ba
FG ta sanar da dalilin da yasa ba za ta bayyana sunayen masu daukar nauyin ta'addanci ba. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC
"Bayyana sunayensu tare da tozarta su ba ya daga cikin dokokin gwamnatin tarayya kuma ba a mutunta hakkin dan Adam ba da ke bayyana gaskiyarsa har sai an kama shi da laifi," takardar ta ce.
"Wannan an yi ne saboda kundin tsarin mulki da kuma doka.Ya na nan a doka kuma za a bayyana sunayen wadanda ake zargin bayan an gurfanar da su.
"Idan akwai shaidu a kasa, dole a mika wanda ake zargi gaban kotu wacce daga nan ne za a bayyana sunayensu. Tozarci kuwa a daya bangaren sai an yanke wa mutum hukunci sannan.
"A takaice dai, bayyana suna da tozarta mai laifi duk alhakin shari'a ne a dokokin Najeriya."

AGF ya kara da cewa, daga cikin fayil din shari'a sama da dubu daya na Boko Haram da sashen gurfanarwa ya samu, an mika 285 gaban wata babbar kotun tarayya.

Kara karanta wannan

EFCC ta kama 'yan damfara ta intanet 30 a jami'ar KWASU

Ya kuma bada tabbacin cewa, masu daukar nauyin ta'addanci da aka gano dole za a gurfanar da su, TheCable ta ruwaito.

Fiye da 'yan Boko Haram 8,000 ne suka mika wuya tare da tuba, GOC

A wani labari na daban, mukaddashin babban kwamandan Div 7, Abdulwahab Eyitayo, ya ce sama da 'yan ta'addan Boko Haram 8,000 ne suka mika wuya ga dakarun sojin Najeriya a Borno.

Ya ce 'yan ta'addan sun mika wuya bayan fitowarsu daga maboyarsu a dajin Sambisa da sauran inda suke boye wa, Premium Times ta ruwaito hakan.

Eyitayo, wanda shi ne kwamandan sashi na 1 na Operation Hadin Kai, ya bayyana hakan yayin ziyarar da daraktan yada labari, Onyema Nwachukwu da wata tawagar tsaro daga Abuja a ranar Talata a Maiduguri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng