'Yan Taliban sun nemi a basu damar gabatar da jawabi a taron da Buhari ya je a Amurka

'Yan Taliban sun nemi a basu damar gabatar da jawabi a taron da Buhari ya je a Amurka

  • Kungiyar Taliban ta nemi ita ma ta halarci taron Majalisar Dinkin da ke faruwa yanzu haka a New York
  • Shugaban kasar Najeriya a halin yanzu yana can kasar Amurka inda ake gudanar da taron na 76 na UN
  • Taliban ta tura wasika, kuma tana jiran amincewa, amma da alamu ba za ta samu abin da take bukata ba

Afghanistan - 'Yan Taliban sun nemi a basu damar shiga cikin shugabannin duniya da ke gabatar da jawabi a zauren Majalisar Dinkin Duniya domin su ma su tofa albarkacin bakinsu, Daily Trust ta ruwaito.

A halin da ake ciki yanzu ana ci gaba da zama na 76 na majalisar dinkin duniya a birnin New York na kasar Amurka.

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari zai gabatar da nasa jawabin ga ilahirin shugabannin duniya a Majalisar Dinkin Duniya a gobe Alhamis 23 ga watan Satumba, 2021.

Kara karanta wannan

Gobara ta yi kaca-kaca da Hedkwatar hukumar NPA, dukiyoyi sun kone kurmus

Taliban sun nemi a basu damar gabatar da jawabi a taron da Buhari ya je a Amurka
Shugabannin Taliban | Hoto: aljazeera.com
Asali: UGC

A wani bangare na kokarin neman amincewar idon duniya, kungiyar Taliban, wacce ta karbe mulki a kasar Afghanistan a hannun tsohon shugaban kasa, Ashraf Ghani a ranar 15 ga Agusta, 2021, ta zabi jakadanta don gabatar da jawabin ga Majalisar Dinkin Duniya.

A cewar mai magana da yawun Majalisar Dinkin Duniya, Stephane Dujarric, Sakatare Janar Antonio Guterres, ya karbi bukatar a ranar 15 ga Satumba daga amintaccen jakadan Afghanistan, Ghulam Isaczai, tare da jerin wakilan Afghanistan don halartar taron.

Dangane da haka, Taliban ta ce tana gabatar da Mohammad Suhail Shaheen a matsayin sabon wakilinta a Majalisar Dinkin Duniya na dindindin.

Shin za a karbi bukatar Taliban?

Har yanzu dai, ba a sani ba tukuna ko kwamitin shaidar sharia na Majalisar Dinkin Duniya zai amince da bukatar wannan kungiya.

Kara karanta wannan

Akwai yuwuwar dan siyasan Najeriya da U.S., UK ke tuhuma ya zama gwamna

Wani jami'i daga kwamitin ya shaida wa kamfanin dillacin labarai na AP a karkashin tsananin sharadin cewa kwamitin na Majalisar Dinkin Duniya "zai dauki lokaci kafin ya yi shawara" kan bukatar ta Taliban

Ya kuma bayyana cewa wakilin Taliban ba zai iya samun damar magana a Babban Taron a wannan zama ba sai dai watakila a wani lokaci nan gaba.

Har zuwa lokacin, a karkashin dokokin Majalisar Dinkin Duniya, Ghulam Isaczai zai ci gaba da zama jakadan Afghanistan a kungiyar ta duniya, in ji Rahoton BBC.

Manyan jami'an ma'aikatar harkokin wajen Amurka sun ce suna sane da bukatar Taliban, amma ba za su iya hasashen yadda kwamitin zai yi hukunci ba.

Mambobin kwamitin sune Amurka, Rasha, China, Bahama, Bhutan, Chile, Namibia, Sierra Leone, da Sweden.

Indonisiya ta yi nadama kan yadda aka ci zarafin jami'in diflomasiyyar Najeriya

A wani labarin, Gwamnatin Indonisiya ta bayyana yin nadama da abin da ya faru da jami’in diflomasiyar Najeriya inda wani bidiyo a shafukan sada zumunta ya nuna jami’anta na shige da fice sun makure shi, BBC Hausa ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yan kudu: Son kai ne Buhari ya yi sansanin sojin ruwa a Kano bai yi a Bayelsa ba

Bidiyon ya nuna yadda jami’in mai suna Abdulrahman Ibrahim wasu maza sun cukuikuye shi a cikin mota.

Najeriya bayan fitar bidiyon ta nuna fushinta tare da yin Allah wadai da abin da ya faru wanda ta ce “ya saba dokar kasa da kasa.”

Sanarwar da ma’aikatar harakokin wajen Indonisiya ta fitar ta ce abin da ya faru ranar 7 ga Agusta 2021 wani abu ne na daban kuma ba zai sauya huldarta da ba da dakatar da ayyukanta na kula da jami’an diflomasiya ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel