Jerin sunaye: Manyan 'yan siyasa 5 da aka kayar a 2019 wadanda ka iya dawowa da karfi a shekarar 2023

Jerin sunaye: Manyan 'yan siyasa 5 da aka kayar a 2019 wadanda ka iya dawowa da karfi a shekarar 2023

Babban zaben shekarar 2019 a Najeriya ya zo da wasu gagaruman matsaloli yayin da wasu manyan 'yan siyasa suka sha mummunan kaye.

Sai dai kuma, yayin da babban zaɓen 2023 ke gabatowa, akwai alamu da ke nuna cewa wasu daga cikin manyan 'yan siyasar da suka sha kaye za su iya dawowa da ƙarfi.

Jerin sunaye: Manyan 'yan siyasa 5 da aka kayar a 2019 wadanda za su iya sake dawowa da karfi a shekarar 2023
Jerin sunaye: Manyan 'yan siyasa 5 da aka kayar a 2019 wadanda za su iya sake dawowa da karfi a shekarar 2023 Hoto: Abubakar Bukola Saraki, Atiku Abubakar, Shehu Sani, Dino Melaye
Asali: Facebook

Ga guda biyar daga cikinsu:

1. Bukola Saraki

A shekarar 2015, Bukola Saraki, tsohon gwamnan jihar Kwara, ya daga inda ya zama mai rike da mukamin siyasa na uku mafi karfin fada a ji a Najeriya, a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.

Sai dai kuma, rikice-rikice da aka gaza magancewa sun sa ya koma tsohuwar jam’iyyarsa ta Peoples Democratic Party (PDP), a shirye -shiryen zaben 2019.

Kara karanta wannan

Gagarumin sako zuwa Kudu maso Gabas: Ku rungumi APC ko ku rasa dama a 2023, Tsohon dan majalisa yayi gargadi

Bayan ya sha kaye a zaben fidda gwani na neman tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a shekarar 2019 a hannun tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, sai Saraki ya yanke shawarar komawa majalisar dattawa.

Sai dai kuma, tsohon shugaban majalisar dattawan ya sha kaye a hannun ɗan takarar APC a zaɓen dan majalisar.

Jam’iyyar APC mai mulki ta kuma samu gagarumar nasara a jihar Kwara, inda ta lashe kujerar gwamna da wasu muhimman kujerun siyasa.

Sai dai da alama Saraki ya dawo kan kafafunsa saboda a yanzu yana taka muhimmiyar rawa a kokarin PDP na kawar da APC mai mulki a shekarar 2023.

Ko ya yanke shawarar komawa Majalisar Dattawa ko ya sake hararar kujerar Shugaban kasa, Saraki zai kasance abun duba a 2023.

2. Shehu Sani

Bayan ya gaza samun tikitin takarar sanatan APC na mazabar Kaduna ta tsakiya a 2019 saboda rikicin sa da gwamna Nasir El-Rufai, Shehu Sani ya bar jam’iyya mai mulki inda ya koma jam’iyyar PRP.

Kara karanta wannan

Hasashe: Garabasa 4 da Shehu Sani kan iya samu ta dalilin komawa PDP

Ya yi takarar kujerar majalisar dattawa a karkashin PRP amma ya sha kaye a hannun dan takarar tsohuwar jam’iyyarsa.

Gabannin 2023, Sanata Sani ya koma PDP a kwanan nan kuma yana iya kwace kujerar sanatan Kaduna ta tsakiya ko ma ya nemi kujerar gwamnan jihar.

3. Dino Melaye

Sanata Dino Melaye, abokin Saraki, shi ma ya koma PDP kafin zaben 2019. Ya fadi kudirinsa na komawa majalisar dattawa ta tara inda abokin hamayyarsa na siyasa kuma dan takarar tsohuwar jam’iyyarsa ta APC, Sanata Smart Adeyemi ya haye kujerar.

Duk kokarin da ya yi na kwato kujerar ta hanyar kotu ya ci tura.

Tun lokacin da ya sha kaye, Melaye ya ci gaba da yin tasiri a siyasance ta hanyar sukar APC da manufofinta akai -akai. A 2023, Melaye na iya kwace kujerar sanatan Kogi ta yamma.

4. George Akume

George Akume, wanda ya kasance tsohon gwamna yana da karfin fada a ji a jihar Benue. Ya taka rawar gani a fitowar Samuel Ortom a matsayin gwamnan Benue a dandalin APC a 2015 (Ortom ya koma PDP).

Kara karanta wannan

2023: Fitaccen dan majalisar arewa ya bayyana dalilin da ya sa APC ke zawarcin Jonathan, ya yi magana akan kudirin Tinubu

Akume wanda ya koma Majalisar Dattawa a 2007 ya sha kaye mai ban mamaki yayin da ya kasa komawa majalisar dattawan a 2019. A 2023.

Baya ga burin komawa majalisar dattawa, a 2023, Akume zai so dawo da APC kan mulki a jihar Benue.

5. Atiku Abubakar

Kudirin Atiku Abubakar na son zama Shugaban kasar Najeriya ya fara ne tun daga shekarar 1992.

Ya tsaya takarar fidda gwani na shugaban kasa na jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) inda ya zo na uku a zaben fidda gwani bayan marigayi Cif Moshood Abiola wanda a karshe ya lashe zaben 12 ga Yuni 1993.

Duk da rasa kujerar sau hudu, tsohon mataimakin shugaban kasar bai yi kasa a gwiwa ba ya yi yunkuri na biyar a 2019. Abin bakin ciki ya sake faduwa.

Akwai rade-radin cewa Atiku zai sake gwada sa’arsa wajen neman shugabancin kasar a karo na shida a 2023.

Kara karanta wannan

2023: APC ta magantu kan rade-radin za ta bai wa Jonathan tikitin takara shugabancin kasa

Arewa za ta cigaba da mulkar Nigeria ko wanene a kujerar shugaban ƙasa, Akintoye

A wani labari na daban, jagorar kungiyar Yarbawa, Farfesa Banji Akintoye ya ce arewa ce za ta cigaba da mulkar Nigeria da mamaye ta koda kuwa wanene ke kan kujerar shugaban kasa.

Ya bayyana hakan ne yayin hirar da aka yi da shi daga Jamhuriyar Nijar a ranar Talata kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Akintoye ya yi wannan furucin ne kwanaki kadan bayan kungiyar dattawan arewa ta ce arewa ba za ta cigaba da sa ido ba a kasar duba da cewa ita ke da yawan al'umma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel