Mun yi nasarar karya lagwan Boko Haram da 'yan bindiga ƙwarai da gaske, Malami

Mun yi nasarar karya lagwan Boko Haram da 'yan bindiga ƙwarai da gaske, Malami

  • Ministan Shari'a, Abubakar Malami ya ce an karya lagwan 'yan ta'adda a Nigeria
  • Malami ya yi wannan jawabin ne yayin zantawa da manema labarai a New York
  • AGF din ya ce kama masu daukan nauyin ta'addanci da aka yi ne ya haifar da nasarorin

New York - Attoni Janar na Nigeria, AGF, kuma ministan shari'a, Abubakar Malami, SAN, ya yi ikirarin cewa an yi nasarar ragargazan 'yan Boko Haram da 'yan bindiga kwarai da gaske, rahoton NewsWireNGR.

Malami ya bayyana hakan ne a birnin New York ta Amurka yayin da ya ke zantawa da manema labarai. Ya kuma yi ikirarin cewa gwamnatin tarayya ta yi nasarar wurin 'binciko da gano wasu manyan mutane' da ake zargi da daukan nauyin 'yan ta'adda a kasar.

Mun yi nasarar karya lagwan Boko Haram da 'yan bindiga ƙwarai da gaske, Malami
Ministan Shari'ar Nigeria, Abubakar Malami. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

Rundunar soji: Muna mutunta su ne kawai, ba tarairayar tubabbun 'yan ta'adda mu ke ba

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar babban jami'in doka na kasar, batun daukan nauyin ta'addanci lamari ne da ake aiki a kansa kuma baya son ya yi magana kan abin da ba a kammala bincike a kansa ba.

Sai dai ya ce:

"Abu daya da zan iya tabbatarwa shine, duba da irin kamen da aka yi, an karya lagwan masu daukan nauyin ta'addanci da 'yan ta'adda don haka za a samu cigaba a bangaren dakile 'yan ta'adda.
"Kana iya gani karara cewa muna samun nasarori kan yaki da Boko Haram, wanda ke nuna cewa ana karya lagwan 'yan ta'addan."

Ya cigaba da cewa:

"Tuni an karya lagwan 'yan ta'addan Boko Haram sosai kuma kana iya ganin abin da ke faruwa a yankin Arewa maso Yamma da ya shafi 'yan bindiga.
"Suma 'yan bindigan an karya lagwan su sosai. Dukkan wannan sakamako ne na abin da muka yi."

Kara karanta wannan

Aikin wutan da ya yi sanadiyyar mutuwar Abba Kyari ya tsaya cak bayan an sa hannu

Sheikh Gumi ya faɗawa Fulani yadda za su yi wa kansu gata a Nigeria

A wani labarin daban, Malamin addinin musulunci mazaunin Kaduna, Dr Ahmad Gumi, ya yi kira ga fulani a su tabbatar sun yi rajista sun kuma karbi katin zabe gabanin babban zaben 2023 da ke tafe a kasar, Daily Trust ta ruwaito.

A cewarsa, samun katin zaben yana da muhimmanci domin hakan zai basu damar zaben shugabanni da za su yi jagoranci na gari sannan su kare musu hakkokinsu.

Gumi ya ce akwai bukatar Fulani su yi rajistan kamar sauran yan Nigeria, domin su zabi mutanen da za su kiyayye musu dabobinsu da dukiyoyinsu da rayukansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel