Siemens: Aikin wutan da ya yi sanadiyyar mutuwar Abba Kyari ya tsaya cak bayan an sa hannu

Siemens: Aikin wutan da ya yi sanadiyyar mutuwar Abba Kyari ya tsaya cak bayan an sa hannu

  • Bincike ya nuna har yanzu aikin Presidential Power Initiative bai je ko ina ba
  • Shekaru biyu da suka ce gwamnatin tarayya ta shiga yarjejeniya da Siemens
  • An ci burin cewa wannan kwangila zai samar da megawatt 25,000 a Najeriya

Abuja - Daily Trust tace shekaru biyu da gwamnatin tarayya da kamfanin Siemens suka sa hannu a yarjejeniyar wutar lantarki, har yanzu ba a fara aiki ba.

Binciken da jaridar tayi ya nuna cewa aikin Presidential Power Initiative (PPI) da ake sa rai zai samar da megawatt 25, 000 na karfin wuta bai kankama ba.

A lokacin da aka sa hannu a wannan yarjejeniya, shugaban kamfanin Siemens AG da ke Jamus, Joe Kaeser yace aikin zai inganta wutar lantarki a Najeriya.

Kara karanta wannan

FG ta sanar da dalilin da yasa ba za ta bayyana sunayen masu daukar nauyin ta'addanci ba

Ya ake ciki yanzu?

Rahoton yace shekaru biyu da aka yi bikin sa hannun fara aikin, babu wani abin da ake iya gani a kasa. Haka zalika babu har yanzu ana fama da karancin wuta.

A wajen wani taro, marubuciyar Najeriya Chimamanda Adichie, ta tambayi shugabar kasar Jamus, Angela Merkel a game da inda aka kwana a kan wannan aikin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Angela Merkel ta maida wa amsa cewa za ta ji daga gare ta, kuma za ta ji inda aka kwana a aikin.

Siemens: Aikin wutan da ya yi sanadiyyar mutuwar Abba Kyari ya tsaya cak bayan an sa hannu
Ana sa hannu a yarjejeniyar Siemens Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Ma’aikatan DisCos da na kamfanin Transmission Company of Nigeria wadanda da su ya kamata a ce an yi wannan aiki sun ce har yau ba a ga komai a kasa ba.

Masana sun ce har yanzu a takarda kurum ake jin labarin aikin, amma babu komai a kasa.

Abba Kyari ya kamu da cuta a Jamus

Kara karanta wannan

Garba Shehu: Saɓani tsakanin gwamnati da ɗan kwangila ne ya hana aikin wutar Mambila

A kokarin ganin aikin PPI ya tabbata ne tsohon shugaban ma’aikatan fadar shugaban Najeriya, Malam Abba Kyari ya kamu da cutar COVID-19 da ya je Jamus.

A karshen wannan cuta ce tayi sanadiyyar mutuwar Abba Kyari a wani asibiti da ke garin Legas.

Jaridar tana ganin sabanin da aka rika samu tsakanin tsohon Ministan wuta, Saleh Mamman da fadar shugaban kasa yana cikin abubuwan da suka jawo cikas.

Idan ba ku manta ba, a ranar 1 ga watan Satumba, 2021, fadar shugaban kasa ta bada tabbacin cewa shugaba Muhammadu Buhari ya kori wasu Ministocinsa.

Wadanda wannan zazzagar ta shafa sune; Alhaji Sabo Nanono da Injiniya Saleh Mamman wadanda ke rike da Ministocin gona da na wuta, Saleh Mamman.

Asali: Legit.ng

Online view pixel