Sheikh Gumi ya faɗawa Fulani yadda za su yi wa kansu gata a Nigeria

Sheikh Gumi ya faɗawa Fulani yadda za su yi wa kansu gata a Nigeria

  • Malamin addinin musulunci mazaunin Kaduna, Sheikh Dr Ahmad Gumi ya shawarci Fulani su mallaki katin zabe
  • Sheikh Gumi ya ce yin rajitsa da samun katin zabe shine hanyar da Fulani za su iya zaben shugabannin da za su kula da hakokinsu
  • Gumi ya kuma yi wa makiyayan gargadi cewa su guji jefa kansu cikin miyagun ayyuka kamar fashi da garkuwa da mutane

Kaduna - Malamin addinin musulunci mazaunin Kaduna, Dr Ahmad Gumi, ya yi kira ga fulani a su tabbatar sun yi rajista sun kuma karbi katin zabe gabanin babban zaben 2023 da ke tafe a kasar, Daily Trust ta ruwaito.

A cewarsa, samun katin zaben yana da muhimmanci domin hakan zai basu damar zaben shugabanni da za su yi jagoranci na gari sannan su kare musu hakkokinsu.

Kara karanta wannan

Malamin addini ya bayyana illar zaɓar miji saboda kyawun sa ba tare da neman zaɓin Ubangiji ba

2023: Ku yi rajista ku mallaki katin zaɓe, Gumi ya yi wa Fulani huɗuba
Sheikh Dr Ahmad Gumi. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gumi ya ce akwai bukatar Fulani su yi rajistan kamar sauran yan Nigeria, domin su zabi mutanen da za su kiyayye musu dabobinsu da dukiyoyinsu da rayukansu.

Ya bukaci Fulani su hada kansu kada su bari 'yan siyasa su raba su, yana mai cewa kabilarsu na da muhimmin rawa da za su taka wurin zaben shugaba na gari a Kaduna da ma Nigeria baki daya.

A ina Gumi ya yi wannan jawabin?

Gumi ya yi wannan jawabin ne yayin mika kayan abinci da dabobi ga iyalan Fulani wadanda rashin tsaro da annobar korona ta shafa wacce wata kungiya mai suna Bilital Marroobe Pastoralists Association of Nigeria (BILMPAN) ta shirya a Kaduna.

Ya ce,

"Idan muna son kuri'un mu su yi tasiri, ya kamata mu hada kai wurin jefa kuri'un mu a zabe mai zuwa. Ya zama dole mu shirya yin aiki tare."

Kara karanta wannan

Zamu Duba Yiwuwar Kafa Dokar Hana Makiyaya Kiwon Fili a Jihar Shugaban Kasa, Gwamna

Babban malamin ya kuma gargadi makiyayan musamman wadanda ke zaune a daji da su guji fashi da garkuwa da mutane.

A cewarsa, karamcin da kungiyar makiyayan ta yi zai taimaka wajen rage wahalhalun da makiyayan ke fuskanta ba tare da jira sai gwamnati ta kawo musu dauki ba.

Tsaro: Gwamnatin Kaduna ta hana yawon gararamba da ayyukan sare itatuwa a dazukan jihar

A wani labarin daban, Gwamnatin Jihar Kana ta haramta yawon 'gararamba' a gari da shiga manyan dazuka a jihar domin yin ayyuka, The Cable ta ruwaito.

Jihar ta kuma hana sare itatuwa domin yin aikin kafinta, girki da gawayi a kananan hukumomi bakwai a jihar saboda karuwar matsalar rashin tsaro.

Kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro na jihar Samuel Aruwan ne ya bada sanarwar a ranar Talata kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel