Mataimakin shugaban ƙasa ya naɗa kansa kyaftin ya shiga fili ya buga wa ƙungiyarsa wasa, an lallasa su 6 - 0

Mataimakin shugaban ƙasa ya naɗa kansa kyaftin ya shiga fili ya buga wa ƙungiyarsa wasa, an lallasa su 6 - 0

  • Mataimakin shugaban kasar Suriname, Ronnie Brunswijk ya shiga fili ya buga wa kungiyarsa wasa
  • Brunswijk mai shekaru 60 ya naɗa kansa kyaftin amma duk da haka an lallasa kungiyarsa 6 - 0
  • Gasar cin kofin CONCACAF dai babban gasa ce don ita ce kwatankwacin Europa League a nahiyar ta North America

Kasar Suriname - Ronnie Brunswijk, mataimakin shugaban kasar Suriname, mai shekaru 60 ya zaɓi kansa don buga wa ƙungiyar ƙwallon ƙafansa wasa a gasar CONCACAF kuma duk da haka sun sha kaye.

Ya nada kansa kyaftin ɗin kungiyar nasa da ya mallaka yayin wasan da aka buga a ranar kamar yadda LailasNews ta ruwaito.

Mataimakin shugaban ƙasa ya naɗa kansa kyaftin ya shiga fili ya buga wa ƙungiyarsa wasa, an lallasa su 6 - 0
Ronnie Brunswijk, mataimakin shugaban kasar Suriname. Hoto: LailasNews
Source: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Jerin sunaye: Manyan 'yan siyasa 5 da aka kayar a 2019 wadanda ka iya dawowa da karfi a shekarar 2023

Brunswijk shine mai kungiyar Inter Moengotapoe kuma shine shugaban kungiyar amma ɗan siyasan ya yanke shawarar ya shiga a fafata da shi a wasarsu na ƙarshe da Olimpia a daren ranar Talata.

Bayan zaben kansa cikin wanda za su buga wasan ya kuma naɗa kansa kyaftin ɗin kungiyar nasa a wasan da aka buga a filin wasa da aka saka wa sunan sa.

Har wa yau, rahoton na LailasNews ya ce ɗan sa Damian shima ya shiga an fafata da shi a wasar amma duk da haka sun sha kaye hannun Olimpia 6 - 0.

Rahotanni game da wasar da aka buga ya nuna cewa Brunswijk ya kammala pas 14 cikin 17 a wasar na mintuna 54.

Gasar ita ce kwatankwacin Europa League a nahiyar ta North America.

Brunswijk ya zama ɗan wasa mafi yawan shekaru da ya buga kwallo a tarihin gasar yana da shekaru 60 da kwanaki 198.

Kara karanta wannan

Gagarumin sako zuwa Kudu maso Gabas: Ku rungumi APC ko ku rasa dama a 2023, Tsohon dan majalisa yayi gargadi

A raba mu, ya ce na cika mugun ci, har rufe kicin yake yi da dare, Firdausi ta yi karar mijinta Haruna a kotu

A wani labarin daban, a ranar Litinin wata Firdausi Sulaiman mai shekaru 23 ta maka mijin ta, Haruna Haruna a gaban kotun musulunci da ke zama a Magajin Gari a Kaduna tana bukatar a raba auren su da shi saboda yadda yake dukanta kamar gangar tashe sakamakon mungun cin abincin ta.

Kamar yadda NewsWireNGR ta bayyana, a korafin da ta yi wa Kotu, Firdausi wacce take zama a Rigasa dake Kaduna ta ce har rufe kicin Haruna yake yi da dare.

Alkalin kotun, Nuhu Falalu, bayan sauraron bangarorin guda biyu, ya dage sauraron shari’ar har sai ranar 4 ga watan Oktoba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164