Gagarumin sako zuwa Kudu maso Gabas: Ku rungumi APC ko ku rasa dama a 2023, Tsohon dan majalisa yayi gargadi

Gagarumin sako zuwa Kudu maso Gabas: Ku rungumi APC ko ku rasa dama a 2023, Tsohon dan majalisa yayi gargadi

  • An yi kira ga mutanen kudu maso gabas da su amince da Jam'iyyar All Progressives Congress a matsayin jam'iyyarsu ta siyasa
  • Victor Ogene ne ya yi kiran inda ya yi iƙirarin cewa ban da wannan, yankin yana cikin haɗarin rashin nasara a 2023
  • A cewarsa, zaben gwamnan Anambra da ke tafe zai sa mutane su sanya kan su cikin yarjejeniyar kasa

Anambra - An aika gagarumin sako ga mutanen kudu maso gabas. Tsohon dan majalisar wakilai kuma jigo a jam'iyyar All Progressives Congress, Victor Ogene ne ya aika da sakon.

Ya yi kira ga mutane da su yarda da APC a yanzu ko kuma su yi hasarar samun tikitin takarar shugabancin kasar nan a 2023, jaridar Punch ta ruwaito.

Gagarumin sako zuwa Kudu maso Gabas: Ku rungumi APC ko ku rasa dama a 2023, Tsohon dan majalisa yayi gargadi
Gagarumin sako zuwa Kudu maso Gabas: Ku rungumi APC ko ku rasa dama a 2023, Tsohon dan majalisa yayi gargadi Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa mai taken ‘Anambra: Dole ne Ndigbo su rungumi APC Yanzu ko kuma su yi hasarar 2023.

Kara karanta wannan

APC za ta wargaje idan aka fito da ‘Dan takarar Shugaban kasa daga Arewa inji Okorocha

A cewarsa, zaben gwamnan jihar Anambra da za a yi a ranar 6 ga Nuwamba, 2021, zai bai wa yankin dama mai yawa don shigar da kansa cikin yarjejeniya ta kasa.

APC za ta wargaje idan aka fito da ‘Dan takarar Shugaban kasa daga Arewa inji Okorocha

A wani labarin kuma, Legit.ng ta rahoto cewa a ranar Litinin, 20 ga watan Satumba, 2021, tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha ya fara nuna tsoronsa game da kai takara Arewacin Najeriya.

Jaridar Punch ta rahoto Rochas Okorocha yana cewa jam’iyyar APC mai mulki za ta bangare kaca-kaca, muddin aka hana ‘yan kudu tikitin shugaban kasa.

Sanata Rochas Okorocha ya kuma ba gwamnati shawarar yadda za ta shawo kan matsalar ta da shugaban haramtaciyyar kungiyar IPOB, Mazi Nnamdi Kanu.

Kara karanta wannan

Shekaru 39 da bada kwangila, ba a soma aikin samar da lantarki a tashar Mambila ba

An rahoto Okorocha ya na kira ga gwamnati ta janye kararta da Nnamdi Kanu, ayi sulhu a wajen kotu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel