‘Yan bindiga sun fi jami’an tsaro yawa a Arewa – Gwamna ya bayyana inda matsalar ta ke

‘Yan bindiga sun fi jami’an tsaro yawa a Arewa – Gwamna ya bayyana inda matsalar ta ke

  • Aminu Bello Masari yace ‘yan bindiga sun zarce jami’an tsaro yawa a Arewa
  • Gwamnan yake cewa wannan ne ya sa Gwamnoni suke daukar ‘yan banga aiki
  • Amma kuma Jami’an tsaro ba su taimaka wa ‘yan sa-kan kamar yadda ya dace

Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari yace ‘yan bindigan da suke ta’adi a Arewacin Najeriya, sun fi jami’an tsaron da ke yankin yawa.

Daily Trust tace Rt. Hon. Aminu Bello Masari ya bayyana haka ne ranar Talata, 21 ga watan Satumba, 2021, lokacin da ya gana da Ministan yada labarai.

Rahoton yace Lai Mohammed ya ziyarci Katsina domin gane wa idanunsa nasarorin da jami’an tsaro ke samu wajen yakar ‘yan bindiga a ‘yan kwanakin nan.

Kara karanta wannan

Jonathan zai yi caca idan ya bar PDP saboda ya samu tikitin 2023 inji Kungiyar Gwamnonin APC

Masari ya tabo jami'an tsaro

Da yake magana, Mai girma gwamnan ya zargi ‘yan sanda da sojoji da kin taimaka wa ‘yan banga.

Aminu Bello Masari yake cewa duka gwamnonin jihohin Arewa sun yi niyyar daukar jami’an sa-kai 3, 000, wadanda jami’an tsaro za su ba horo da kayan aiki.

Masari
Gwamnan Katsina, Aminu Masari Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

“Amma labarin da nake samu na wannan aiki a Katsina shi ne ba a ba ‘yan sa-kan goyon-baya.”
“Bari in saki layi kadan domin in yi magana a kan ‘yan sanda da sojoji. Muna so a kawo ‘yan sa-kai da za su koya wa aiki, amma kuma an ki ba su goyon-baya.”
“Mun samu kan mu a wani hali da adadin ‘yan bindiga ya zarce na jami’an tsaro. Idan aka samu ‘yan banga da aka yi wa horo da za su bada agaji, zai taimaka.”

Kara karanta wannan

‘Yan bindigan da aka fatattako daga Zamfara sun tare hanyoyin Katsina suna neman abinci

Wani kokari Gwamna Masari yake yi?

Aminu Masari yace gwamnati za ta kara daukar wasu ‘yan sa-kai 500, masarauta ma za ta dauki mutane 250 wadanda ake sa rai a koya wa aiki, su kare jama’a.

Daga cikin kokarin da gwamnatin Katsina ta ke yi, Rt, Hon. Masari yace an rufe kasuwannin dabbobi, an hana saida gwanjon babur domin a magance matsalar.

Gurgu: Ka fi mai kafa iya shege

A makon nan ne jami'an 'yan sandan jihar Katsina suka yi ram da wani gurgu mai shekaru 22 mai suna Buhari Haruna da ake zargi yana cikin masu satar mutane.

Kakakin rundunar 'yan sanda na Katsina, SP Gambo Isah, yace an kama Haruna ne yayin da ya je karbar kudin fansan kuma yayi basaja ta yadda ba za a gane shi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel