Jonathan zai yi caca idan ya bar PDP saboda ya samu tikitin 2023 inji Kungiyar Gwamnonin APC

Jonathan zai yi caca idan ya bar PDP saboda ya samu tikitin 2023 inji Kungiyar Gwamnonin APC

  • Ana jita-jitar Dr. Goodluck Jonathan zai bar Jam’iyyar PDP, ya dawo APC
  • Shugaban PGF, Salihu Lukman ya yabi tsohon Shugaban kasa, Dr. Jonathan
  • Jigon na APC yayi kira ga APC ta zauna kan yadda za ta fito da ‘dan takara

Abuja - Darekta Janar na kungiyar Progressive Governors’ Forum, Salihu Mohammed Lukman, ya yi magana kan koma war Goodluck Jonathan APC.

Daily Trust tace Salihu Mohammed Lukman ya tofa albarkacin bakinsa ganin ana ta rade-radin cewa tsohon shugaban Najeriyar zai iya sauya-sheka.

Lukman ya fitar da jawabi a ranar Lahadi, 19 ga watan Satumba, 2021, yana kiran kusoshin APC su zauna, su tsara yadda babban zaben 2023 zai kasance.

Jawabin Salihu Mohammed Lukman

“A matsayinmu na ‘ya ‘yan APC, mun yi yaki domin hana Jonathan koma wa mulki a 2015. A matsayinsa na shugaban kasa, ya nemi ya hana a kafa APC a 2023.”

Kara karanta wannan

Jigon APC a Kano ya yi tir da tarbar da Buhari, APC suka yi wa Fani-Kayode a fadar Aso Villa

“Amma ba wadannan ya kamata a duba ba. Abin da ya kamata a lura shi ne yadda shugaba Jonathan ya sallama zaben 2015 tun kafin a kammala tattara kuri’u.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jonathan
Goodluck Jonathan yana kamfe a Bauchi Hoto: www.nairaland.com
Asali: UGC

“Da wannan Jonathan ya sa kan shi cikin wadanda suka kare damukaradiyyar kasar. Saboda haka ka da a bari wata jam’iyya tayi kokarin toshe tauraruwarsa.”
“Yin hakan yana nufin watsi da gagaruman nasarorin da ya samu. Ya isa abin takaici ganin yadda shugabannin PDP ba su girmama darajar Jonathan a siyasa.”

Darektan PGF, Alhaji Lukman ya bukaci manyan APC su fito da dabarar lashe zabe mai zuwa.

Kamar yadda jaridar ta fitar da rahoto, abin da Lukman yake so APC ta yi shi ne ta fito da yadda za a tsaida wanda za a ba takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

2023: Fitaccen dan majalisar arewa ya bayyana dalilin da ya sa APC ke zawarcin Jonathan, ya yi magana akan kudirin Tinubu

Lukman ya yi tir da yadda wasu shugabannin APC suka hada-kai da ‘yan jam’iyyar adawa ta PDP, suna kiran a maida shugabanci ya koma kudancin Najeriya.

Jigon APC ya soki shugabannin Arewa

A jiya Muaz Magaji ya maida martani bayan an karbi Femi Fani-Kayode a jam'iyyar APC. Magaji yace ya rasa gane manufar APC ganin yadda ta karbi tsohon 'dan adawar.

Shugaban Win-Win ya yi ta maganganu a Facebook, yana sukar sauya-shekar Fani-Kayode.

Asali: Legit.ng

Online view pixel