Wasu ‘Yan bindigan da aka fatattako daga Zamfara sun tare hanyoyin Katsina suna neman abinci

Wasu ‘Yan bindigan da aka fatattako daga Zamfara sun tare hanyoyin Katsina suna neman abinci

  • ‘Yan bindiga sun tsare wasu hanyoyi a Katsina suna tsare Bayin Allah
  • Ana zargin wadannan ‘yan bindiga sun fito ne daga jejin jihar Zamfara
  • Mazauna yankin sun ce wadannan miyagu suna neman fetur da abinci

Zamfara - Mazauna wasu kauyukan karamar hukumar Kankara a jihar Katsina sun ankarar da jama’a game da shigo war ‘yan bindiga a yankin.

Daily Trust ta kawo rahoto a ranar Juma’a, 17 ga watan Satumba, 2021, cewa an ga ‘yan bindigan da sojoji suka koro daga Zamfara a jihar Katsina.

Majiya tace an ga wadannan ‘yan bindiga a cikin zuga suna tsere wa daga kauyukan na garin Kankara.

Wani mazaunin kauyen Pawwa ya shaida wa jaridar a ranar Juma’a cewa ‘yan bindigan sun kafa shinge, sun tare hanyoyi suna tare masu wuce wa.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: Mun cafke mutum fiye da 100 da ke ba ‘Yan bindiga bayanai a Zamfara - Matawalle

‘Yan bindigan suna karbar dukiyar mutanen da hanya ta hada su da bin titin Kankara zuwa Zango.

Da aka tuntubi kakakin ‘yan sanda na jihar Katsina, Gambo Isah, yace ana kokarin zuzuta lamarin.

Sojoji
Sojojin Najeriya a bakin aiki Hoto: www.pulse.ng
Asali: UGC

Abin da mazauna gari suke fada

“Babban abin da ke damun su shi ne abinci da man fetur. Suna dauke da robobi da suke karbar fetur daga masu abin hawa, suna kuma karbar abinci.”

A cewar mazaunin wannan yanki na Pawwa, duk inda ‘yan bindigan suka samu abinci, dauka suke yi. Alamar cewa sun baro jejin Zamfara cikin yunwa.

“Kusan kwana biyu da suka wuce, suka tare wata babbar mota da ta dauko kayan abinci, suka dauke duka hatsin da ke cikin motar, suka yi gaba.”

Haka zalika wani mutumi da ke zaune a yankin, ya tabbatar da wannan labari, yace suna da sanar da jami’an tsaro cewa suna fuskantar barazana a yanzu.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun ce tsohuwa tukuf mai shekara 86 ta biya N20m kafin a fito da 'Danta da Jikoki 3

Tsoron mazauna yankin shi ne dama can suna fama da ‘yan bindiga, sai kuma yanzu ga karin wasu da ake zargin sun tsere ne daga kauyukan jihar Zamfara.

An cafke wani 'Dan bindiga a Kaduna

An samu labari cewa 'yan sannda sun kama wani mutumin Zamfara wanda da hannun shi ne aka dauke ‘Yan makarantar gwandu, Bethel da Jami’ar Greenfield.

Jami’an ‘Yan Sandan jihar Kaduna sun shaida cewa wannan mutumi ya amsa laifuffukansa da kansa. Ana zarginsa da garkuwa da mutane a yankin Giwa da Igabi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel