'Yan sanda sun yi ram da gurgu mai shekaru 22 kan zargin garkuwa da mutane

'Yan sanda sun yi ram da gurgu mai shekaru 22 kan zargin garkuwa da mutane

  • Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da damke wani matashin gurgu mai shekaru 22 a duniya
  • Ana zarginsa da yunkurin garkuwa da makwabcinsa inda ya bukaci a biya shi miliyan 2 ko ya sace shi
  • Gurgu Haruna Buhari ya amsa laifinsa inda ya ce a duba nakasarsa a yi masa rangwame kuma ya yi nadama

Kankia, Katsina - Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta yi ram da wani matashin gurgu mai shekaru 22 mai suna Buhari Haruna daga karamar hukumar Kankia ta jihar.

Ana zargin gurgu Buhari Haruna da barazanar sace wani idan ba a biya shi kudi har naira miliyan biyu ba, LIB suka ruwaito.

'Yan sanda sun yi ram da gurgu mai shekaru 22 kan zargin garkuwa da mutane
'Yan sanda sun yi ram da gurgu mai shekaru 22 kan zargin garkuwa da mutane. Hoto daga lindaikejiblog.com
Asali: UGC

A yayin damke wanda ake zargin tare da nunawa manema labarai, kakakin rundunar 'yan sandan, SP Gambo Isah, ya ce an kama Haruna ne yayin da ya je karbar kudin fansan kuma yayi basaja kamar sunkin biredi a wurin da aka yi za a karba.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Wani jirgin yaki ya yi luguden wuta a Yobe ya kashe fararen hula da dama

Isah ya ce, kamen Haruna ya bayyana cewa, hatta wadanda ba a tsammanin za su yi laifi a yanzu suna amfani da mummunar damar wurin satar jama'a.

A yayin jawabi ga manema labarai bayan kamensa, Haruna bai musanta laifin da ake zarginsa ba.

Ya ce ya kira mutumin da ke makwabcinsa ne tare da yi masa barazanar cewa in har bai biya kudi naira miliyan biyu ba, zai yi garkuwa da shi.

Ya ce ya yi nadamar abinda ya yi, duk da shi mai nakasa ne, ya na rokon yafiya kuma 'yan sandan su yi masa rangwame, LIB ta ruwaito.

'Yan ta'addan ISWAP sun fara gangamin diban jama'a aiki, Rundunar sojin kasa

A wani labari na daban, Onyema Nwachukwu, mai magana da yawun rundunar sojin kasa ta Najeriya, ya ce 'yan ta'addan ISWAP sun fara gagarumin gangamin diban jama'a domin zama mambobinsu.

Kara karanta wannan

Ba zan sake soyayya ba, cewar dan sadan da budurwa ta yaudara bayan ya kashe mata kudin makaranta

Kamar yadda TheCable ta ruwaito, rundunar sojin ta kaddamar da hare-hare kan miyagun 'yan ta'addan karkashin Operation Hadin Kai a yankin arewa maso gabasa ta kasar nan.

Daruruwan 'yan ta'adda da suka hada da manyan kwamandojinsu sun mika wuya ga dakarun sojin Najeriya a makonni kalilan da suka gabata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng