Shekaru 39 da bada kwangila, ba a soma aikin samar da lantarki a tashar Mambila ba

Shekaru 39 da bada kwangila, ba a soma aikin samar da lantarki a tashar Mambila ba

  • Shekaru kusan 40 da bada kwangilar Mambila, har yanzu babu abin da aka tabuka
  • Idan aikin ya kammala, Najeriya za ta samu karin karfin wuta na megawatt 3, 000
  • A halin yanzu mutane miliyan 200 a kasar suna raba megawatt 5,000 zuwa 5400 ne

Taraba - BBC Hausa ta gudanar da wani bincike na musamman a kan tashar wutar lantarkin Mambila inda ta gano cewa har yau ba a soma wannan aikin ba.

Shekara 39 kenan da gwamnatin shugaba Shehu Shagari ta bada kwangilar samar da wutar lantarki ta tashar Mambila, kawo yanzu babu labarin wannan aiki.

A shekarar 1982 aka tsara cewa tashar za ta samar da megawatt 2600 na karfin wuta idan an gama aikin.

Kara karanta wannan

Sarki a Arewacin Najeriya ya ce mata su karbi mulki a hannun Buhari a 2023 kawai

Amma da ‘dan jaridar BBC ya ziyarci tashar, sai ya gano cewa ba a fara yin aikin ba. ‘Dan jaridar ya je har gangaren ruwa na Tambi wanda yana cikin tsarin tashar.

Duk da cewa mota ba ta iya zuwa wannan wuri, ‘dan jaridar ya hau babur, inda ya shafe sa’o’i biyar yana tafiya, daga baya sai ya karasa tashar lantarkin a kafa.

Tashar Mambila ba
Tashar Mambila a Taraba Hoto: nairametrics.com
Asali: UGC

Shekara da shekaru babu labari

Shugabanni goma aka yi a Najeriya amma ba su iya cika alkawarin da aka yi ba. Shugabannin su ne; Shehu Shagari, Muhammadu Buhari da Ibrahim Babangida.

Sai Ernest Shonekan, Sani Abacha da Abdussalami Abubakar. Daga nan sai Olusegun Obasanjo, Ummaru ‘Yar’adua, Goodluck Jonathan sai Buhari (ya dawo).

Har yanzu aiki bai kankama ba?

Kara karanta wannan

Shugaban EFCC ya yanki jiki ya fadi yayin da yake magana a dakin taro

Rahoton yace mafi yawan hotunan da ake gani a shafukan yanar gizo a kan wannan aiki, na bogi ne.

Mutane suna dauko hotunan takwarar tashar Mambila, madatsar ruwar Kashimbila (duk a jihar Taraba), suna yada wa da sunan tashar wutar lantarkin Mambila.

A wata hira da aka taba yi da Injiniya Saleh Mamman a lokacin yana Ministan wutar lantarkin Najeriya, yace batun wannan aikin tamkar tatsuniya ce kurum.

Buhari ya kori Ministan wuta

Daga baya an ji cewa shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sauke ministan noma da ministan harkar wutar lantarki Saleh Mamman bayan shekaru biyu a ofis.

Saleh Mamman ya yi magana a shafinsa na Facebook bayan an kore shi daga mukamin Minista. Mamman ya gode da damar da aka ba shi a gwamnatin tarayya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel