Saleh Mamman ya yi magana a Facebook, awa 24 bayan Buhari ya tunbuke shi daga Minista
- Shugaban Kasa ya sauke ministan noma da ministan harkar wutar lantarki
- Saleh Mamman ya yi magana a shafinsa na Facebook bayan an sallame shi
- Tsohon Ministan ya gode da damar da aka ba shi har na tsawon shekara biyu
Abuja - Bayan an tabbatar da sallamar shi daga Ministan harkar wutar lantarki, Injiniya Saleh Mamman yace ya samu nasarori sosai da yake ofis.
Saleh Mamman ya yi amfani da Facebook a ranar Alhamis, 2 ga watan Satumba, 2021, ya gode wa wadanda suka taimaka aka yi nasara a bangaren wuta.
Buhari ya bani damar rike Minista
Injiniya Mamman ya fara da nuna godiyarsa ga Ubangiji da kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari, da ya ba shi damar rike wannan babban mukami.
A cikin kan-kan da kai da fawwala lamari ga Allah, tsohon Ministan ya gode da aka ba shi dama ya bada irin na sa gudumuwar a gwamnatin tarayya.
“Na ji dadin yarda da ni da imani da ni da yayi (yana nufin Buhari), musamman taimakon da ya bani a lokacin da nake rike da kujerar Ministan wuta."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Punch ta rahoto jawabin tsohon Ministan, inda aka ji yana godiya ga Farfesa Yemi Osinbajo da duka sauran Ministocin da suka yi tare na shekaru biyu.
Duk da ya bar ofis, Mamman yace zai cigaba da bada gudumuwa domin Najeriya ta cigaba, baya ga nasarorin da ya samu da yake rike da ma’aikatar.
Saleh Mamman ya gode wa Osinbajo
“Zan cigaba da jajircewa domin ganin cigaban kasarmu Najeriya, za mu cigaba da bada goyon baya.”
“Ina kuma mai godiya ga Mai girma mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo da sugabancin da ya yi a kwamitin sa ido na gyaran wuta."
“Ga abokan aiki na a majalisar zartarwa, ina mika godiya na hadin-kai da muka samu wajen aiki tare, da kuma zumuncin da aka kulla a sanadiyyarsa.”
...Duk bula ce - Elumelu
Majalisar ‘yan adawa a majalisar wakilan tarayya sun ce wasan yara shugaba Muhammadu Buhari ya yi da ya yi waje da Saleh Mamman da Sabo Nanono.
Hon. Ndudi Elumelu yace da a kori Ministoci, gara a shawo kan harkar tsaro da tattalin arziki. A cewarsa, an sauke Ministocin biyu ne domin a yaudari al'umma.
Asali: Legit.ng