Sarki a Arewacin Najeriya ya ce mata su karbi mulki a hannun Buhari a 2023 kawai

Sarki a Arewacin Najeriya ya ce mata su karbi mulki a hannun Buhari a 2023 kawai

  • Sarkin Keffi ya shawarci mata kan cewa su daga murna su shiga siyasa a zabe mai zuwa na 2023
  • Ya bayyana cewa, idan har mata za su iya shugabancin gida, to lallai za su iya shugabancin kasa
  • Ya bayyana haka ne yayin ganawa da wasu shugabannin mata da ke fafutukar kafa gwamnatin mata

Nasarawa - Mai martaba Sarkin Keffi, Alhaji Shehu Yamusa III, ya yi kira ga matan Najeriya da su nuna sha’awarsu ta shugabancin kasa domin su gaji shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a shekarar 2023, yana mai cewa hakan ba zai gagara ba.

A cewarsa, ‘yan Najeriya, ba tare da la’akari da kabila ko alakar siyasa ba, dole ne su raba tunanin al’adu da siyasa don samar da mafi kyawun shugabanci a kasar, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shugaban EFCC ya yanki jiki ya fadi yayin da yake magana a dakin taro

Sarkin, wanda kuma shi ne Shugaban Jami'ar Jihar Nasarawa, ya yi wannan furuci ne a ranar Alhamis 16 ga watan Satumba.

Sarki a Arewacin Najeriya ya ce Buhari ya damkawa mace mulki a zaben 2023 kawai
Sarkin Keff ta jihar Nasarawa | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Ya bayyana haka ne lokacin da mambobin tafiyar 'National Democratic Institute International Working Group for Supporting the Advancement of Gender Equality Programme', suka ziyarce shi a fadarsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daga cikin tawagar akwai shugabar mata ta farko a Jamhuriyar Kosovo dakuma shugabar tawagar SAGE ta NDI, Madam Atifete Jahjaga.

Yamusa ya ce:

“Mafi mahimmanci, zan so in jawo hankalin daukacin al’umma kan cewa al’adu da siyasa abubuwa biyu ne daban. Sau da yawa muna kuskuren gama su ga juna, kuma wannan shine dalilin da ya sa yawancin mata ba za su iya fitowa don yin takarar mukamai a siyasa ba Amma suna cikin mu, kuma dole ne mu tafi tare dasu.

Kara karanta wannan

An saki bidiyo yayin da kwamandan IPOB/ESN Shakiti-Bobo ya ambaci sunan mai daukar nauyin kungiyoyin

“Duba da kokarin su a cikin gidajen mu daban-daban, ina ganin ya kamata mu ba su dama a babban zabe mai zuwa. Idan mata za su iya sarrafa iyalai, za su iya sarrafa kasa.”

Don haka, ya jaddada bukatar dukkan 'yan siyasa su girmama matsayin mata a fafutukar neman mulki kamar yadda dukkan kowa ke da wani abu da zai iya bayarwa na gudunmawa a kasa.

Basaraken ya ci gaba da bayyana cewa mata za su iya samar da irin shugabanci da Najeriya ke bukata ta hanyar tallafa wa junansu don cin zabe a 2023, da kuma tabbatar da ingantaccen gudanarwa da rarraba albarkatun kasa daidai.

Jahjaga ta tabbatar da hakkokin mata na shiga siyasa da wakilci a albarkatun tattalin arziki tare da samun tsaro da adalci.

Ta kuma yi kira da a dauki kwararan matakai don tabbatar da wadannan ka'idoji a Najeriya.

Ta ce:

"Muna da manufa don tallafa wa gwamnati da jama'ar Najeriya ta hanyar ba da gudummawa ga yawan mata a cikin siyasa, aiki a cikin hanyar karfafa jinsi."

Kara karanta wannan

Shugabancin 2023: Okonjo-Iweala, Peter Obi da wasu 'yan siyasa 16 na kudu maso gabas da aka nemi suyi takara

2023: Shin Tinubu zai gaji Buhari? Sanannen sanatan arewa ya fede biri har wutsiya kan mulkin karba-karba

Tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Sanata Abdullahi Adamu, ya gaya wa wadanda ke kira ga mika shugabanci zuwa yankin kudancin ƙasar a 2023 da su binne tunaninsu.

Jaridar Punch ta rahoto cewa Adamu wanda shine sanata mai wakiltar yankin Nasarawa ta yamma a majalisar tarayya ya bayyana mulkin karba-karba a matsayin wanda ya sabawa kundin tsarin mulki.

Legit.ng ta tattaro cewa tsohon gwamnan na sau biyu ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai a Abuja a ranar Litinin, 13 ga watan Satumba.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa tsohon gwamnan na Nasarawa ya ce duk da cewa akwai kiraye-kirayen da ake yi na mika kujarer shugaban kasa ga shiyyar kudu maso gabas, amma babu wani tanadi na tsarin mulki kan hakan.

A cewarsa, tunda ra'ayin karba-karba ba ya cikin kundin tsarin mulkin kasar, kowane dan Najeriya da ya cancanta yana da 'yancin tsayawa takarar shugaban kasa a 2023 ba tare da la’akari da jiharsa ta asali ba.

Kara karanta wannan

Shugabannin Boko Haram matsorata ne: Tubabben kwamandansu ya tona asiri

Jiga-jigan APC sama da 30 suna harin kujerar Ministan wutan lantarki da aka tsige

A wani labari na daban, akalla jagororin jam’iyyar APC 32 a jihar Taraba suna neman maye gurbin Saleh Mamman, wanda aka tsige daga mukamin Ministan wuta. J

aridar Daily Trust tace manyan ‘yan siyasan Kano da Taraba inda Sabo Nanono da Injiniya Saleh Mamman suka fito, suna hangen kujerun Ministocin tarayya.

Ana sa rai shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tura sunayen wadanda za su maye guraben Ministocin da ya kora da zarar ‘yan majalisa sun dawo aiki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel