2023: APC ta magantu kan rade-radin za ta bai wa Jonathan tikitin takara shugabancin kasa

2023: APC ta magantu kan rade-radin za ta bai wa Jonathan tikitin takara shugabancin kasa

  • Jam’iyyar APC ta ce bata bai wa Goodluck Jonathan tabbacin samun tikitin takarar shugaban kasa ba kamar yadda ake ta yadawa
  • Dama ana ta yada cewa ya na shirin komawa APC ne don ya tsaya takarar shugaban kasa a zaben 2023 da yake gabatowa
  • Sakataren rikon kwaryar jam’iyyar APC na kwamitin tsare-tsare, CECPC, John Akpanudoedehe, ya sanar a ranar Juma’a a Abuja

Abuja - Jam’iyyar APC ta ce ba ta tabbatar wa da tsohon shugaban kasan Najeriya, Goodluck Jonathan tabbacin tikitin tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023 ba, kamar yadda ake ta yadawa.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, sakataren CECPC, John Akpanudoedehe ya bayyana hakan a wata takarda a Abuja ranar Juma’a.

Ya ce komawar mutum jam’iyya ba ya bayar da tabbacin a bashi wani matsayin a jam’iyya.

Kara karanta wannan

'Kwararan Dalilan Da Suka Sa Tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan Ke Jinkirin Komawa Jam’iyyar APC

2023: APC ta magantu kan rade-radin za ta bai wa Jonathan tikitin takara shugabancin kasa
2023: APC ta magantu kan rade-radin za ta bai wa Jonathan tikitin takara shugabancin kasa. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Akpanudoedehe ya yi karin haske ne a kan sauya fahimtar sa da aka yi na rangwamen da NEC ta bai wa sababbin mambobin jam’iyya da masu sauya sheka a wani taron su da suka yi a ranar 8 ga watan Disamban 2020.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yayin wani shirin gidan talabijin, ya ce duk wani dan jam’iyya komai matsayin sa sai ya bi dokar zabe wanda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadar.

Ya tsaya akan batun rangwamen NEC ba zai tsaya a kan kowa ba, Daily Nigerian ta wallafa.

Kamar yadda sakataren ya ce:

“Rangwamen zai shafi kowa da kowa ba kamar yadda mutane suke canja maganar ba.
“Ba za a fifita mutum a bashi wani matsayi na daban ba har da damar tsayawa takara kawai saboda sabon dan jam’iyya ne. Duk mai neman takara dole ne ya bi duk tsarin da kundin tsarin mulkin APC ya tanadar.”

Kara karanta wannan

Rikicin APC: Kamata ya yi a dawo da ni kan hanya idan na kauce, Gwamnan Gombe

Akpanudoedehe ya tunatar da yadda NEC din jam’iyya ta shirya bayar da rangwame ga sababbin ‘yan jam’iyya da masu burin shiga jam’iyyar don ya tsaya takarar wani matsayi a jam’iyyar APC kasancewar ita ce jam’iyyar da ake yayi a halin yanzu.

Ya bayyana cewa batun da NEC tayi na , “APC za ta samar wa sababbin ‘yan Jam’iyya matsayi na musamman sai dai ba tikitin tsayawa takara ba.”

A cewar sa:

“A wata tattaunawa da aka yi da ni a gidan talabijin a kan maganar da tayi ta yaduwa a kan Goodluck Jonathan zai koma jam’iyyar APC, magana ta ita ce NEC ta tabbatar da bai wa sababbin ‘yan jam’iyya rangwame na daban.
“Sai dai rangwamen ba a kebantar da shi ga wasu mutane na daban ba kamar yadda mutane su ka yi ta yadawa. Duk mai neman matsayi zai dage ya bi dokokin da kundin tsarin APC ya tanadar.

Kara karanta wannan

APC ta kare Buhari, ta fadi dalilan gwamnatin tarayya na karbo bashin tiriliyoyi bini-bini

Asali: Legit.ng

Online view pixel