'Kwararan Dalilan Da Suka Sa Tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan Ke Jinkirin Komawa Jam’iyyar APC

'Kwararan Dalilan Da Suka Sa Tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan Ke Jinkirin Komawa Jam’iyyar APC

  • Wata majiya mai karfi ta bayyana dalilan da suke dakatar da Jonathan daga komawa jam’iyyar APC a halin da ake ciki
  • An bayyana cewa masu juya mulkin Buhari suna so Jonathan ya maye gurbin sa idan ya sauka don ba zai yi bincike akan su ba
  • Wannan dalilin ne yasa Jonathan ya dakata har su tunkude burin Tinubu na tsayawa takara sai ya koma ya maye gurbin sa

Akwai kwararan dalilan da suke ta dakatar da tsohon shugaban kasan Najeriya, Goodluck Jonathan daga komawa jam’iyyar APC mai mulki a kasa.

Sahara Reporters ta ruwaito yadda manyan ‘yan jam’iyyar APC masu juya mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari suke son janyo Jonathan zuwa jam’iyyar APC don kada burin jagoran jam’iyyar na kasa, Bola Tinubu na zama shugaban kasa a shekarar 2023 ya tabbata.

Kara karanta wannan

APC ta kare Buhari, ta fadi dalilan gwamnatin tarayya na karbo bashin tiriliyoyi bini-bini

'Kwararan Dalilan Da Suka Sa Tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan Ke Jinkirin Komawa Jam’iyyar APC
Tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan. Hoto: The Punch

Ana tsaka da yada rahotanni akan burinsa na komawa APC daga jam’iyyar PDP, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya dan dakata ne sakamakon wasu sharuddan da yake jira APC ta cika.

SaharaReporters ta bayyana yadda baya ga wannan dalilin, masu juya mulkin Muhammadu Buhari suke fargabar son kawo Jonathan don su lalata shirin jagoran jam’iyyar na kasa, Bola Tinubu na zama shugaban kasan Najeriya a 2023.

Wata majiya mai karfi ta sanar da SaharaReporters cewa Buhari ya yita neman Jonathan ya koma APC tun 2020 don ya maye gurbin sa idan ya sauka.

Majiyar ta ce, ‘yan fadar shugaban kasa suna so Jonathan ya dare mulki bayan Buhari ya sauka don sun san ba zai tsananta binciken lamurran da suka auku ba a lokacin mulkin Buhari.

Kara karanta wannan

A'isha Buhari: Dalilin da ya sa na wallafa bidiyon Pantami yana rusa kuka yayin wa'azi

Kowa ya san yadda Jonathan ya dade yana so ya koma kujerar don kammala karon sa na 2, damar da APC ta hana shi sakamakon mummunan kayen da ta yi masa a zaben 2015.

Sai dai ya hakura ya mika wuya musamman ganin cewa baya da tabbacin tsayawa takara a PDP musamman ganin yadda tsohon shugaban kasa Atiku Abubakar ya fi shi kudi da sanin jama’a yake da burin tsayawa takara.

Duk da Atiku bai bayyana ra’ayin sa na tsayawa takara ba, Jonathan ya na zullumi

A zaben 2019, dama Atiku ne ya tsaya takarar shugabancin kasa a lokacin. Duk da dai har yanzu Atiku bai tsaya ya bayyana ra’ayin sa na tsayawa takara a 2023 ba amma akwai alamun hakan.

Sannan Jonathan yana fargaban yadda gwamna Tambuwal na jihar Sokoto da gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers suke kokarin tsayawa takara a jam’iyya PDP, ko wannan ma kalubale ne a gare shi.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Jam'iyyar APC ta fatattaki tsohon gwamna da wasu mambobi 40

Don haka ne har yanzu Jonathan ya bai wa masu juya gwamnatin Buhari wasu sharruda da har yanzu basu riga sun cika ba shiyasa har yanzu bai koma jam’iyyar APC ba.

Jonathan ya san da kyar PDP ta tsayar da shi a matsayin dan takarar shugaban kasa a 2023

Kamar yadda majiyar ta ce:

“Kusan shekara daya kenan da Jonathan ya fara tuntuba yana neman yadda ze yi ya koma APC. Jonathan ya san cewa da kyar ya samu damar tsayawa takara a PDP sakamakon yadda Atiku, wanda ya fi shi mutane da dukiya yake neman kujerar sannan Tambuwal da Wike ma sun nuna ra’ayin su akan tsayawa takarar."

Ganin yadda masu juya mulkin Buhari suke so su jefi tsuntsu biyu da dutse daya, wato su tunkudar da burin Tinubu na maye gurbin Buhari a 2023 sannan su maye shi da Jonathan wanda za su ci karen su babu babbaka yasa ya dakata har zuwa wani lokaci.

Kara karanta wannan

Jigon APC ya bayyana wanda ya dace da mulki, ya cire Osinbajo, Tinubu a lissafin 2023

Majiyar ta kara da cewa:

“Buhari da masu juya mulkin sa suna so su dakatar da takarar Tinubu su dauki Jonathan.“

A ƙarshe, APC ta yi magana kan raɗe-raɗin Goodluck Jonathan zai shigo jam'iyyar

A wani labarin daban, Jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a ranar Laraba ta ce za ta karbi tsohon shugaban kasar Nigeria, Goodluck Jonathan idan yana da sha'awar shigowa jam'iyyar, The Punch ta ruwaito.

Ta kuma ce zai kuma mora duk wani alfarma da gata kowanne dan jam'iyyar ke da shi ba tare da la'akari da lokacin da ya shigo jam'iyyar ba.

A cewar rahoton na The Punch Sakataren jam'iyyar na kasa, Sanata John Akpanudoedehe ne ya bayyana hakan yayin da ya ke amsa tambayoyi a shirin Channels Television mai suna Politics Today.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164