Rikicin APC: Kamata ya yi a dawo da ni kan hanya idan na kauce, Gwamnan Gombe
- Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na Jihar Gombe ya ce a dawo da shi hanya idan an ga ya kauce
- Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin tsokaci a kan rikici shugabannin jam’iyyar APC na jihar Gombe
- Ya kuma musanta batun akwai fadan neman mulki tsakanin sa da tsohon gwamnan jihar, Danjuma Goje
Gombe - Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya ce a dawo da shi hanya idan an ga ya kauce.
Daily Trust ta ruwaito cewa, Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin yin tsokaci dangane da rikicin shugabancin jam’iyyar APC a jihar.
Ya musanta batun samun rikicin shugabanci tsakanin sa da tsohon gwamnan jihar, Danjuma Goje, Daily Trust ta ruwaito hakan.
Gwamnan ya sanar da BBC cewa, ba ya da wani takun-saka tsakanin sa da Goje, sai dai wajibi ne kowa ya yi biyayya ga tsarin shugabancin jam’iyya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yahaya ya warware sarkakiyar da ake ta cewa suna da wata kulalliya tsakanin sa da Goje.
A wata tattaunawa da BBC ta yi da Yahaya, ya musanta zargin da ake masa inda ya ce jam’iyyar sa ta bayyana matsayin ta.
“Ba na da wata rashin jituwa da shi, sai dai jam’iyya ce za ta bai wa kowa dama sannan ya kasance mai gaskiya,” a cewar sa.
“Mu ‘yan jam’iyya ne; dole ne a bi tsarin jam’iyyar... Idan na kauce hanya a gyara min saiti na, duk wanda aka ga ya kauce hanya, a yi masa gyara.”
Yayin da ya bayyana matsayin sa a rikicin cikin gida na jam’iyyar APC, gwamnan ya ce gara matsalolin jam’iyyar su a jihar Gombe a kan ta wasu jihohin.
Batun tsarin karba-karbar shugabancin jam’iyya da kudu, “batun tsarin cikin gida ne”.
“Ba zai taba zama babbar matsala ba a nan gaba- a harkar siyasa, kowa ya na da damar shugabanci ,” a cewar sa.
IGP ya nada sabuwar mai magana da yawun rundunar 'yan sandan FCT
A wani labari na daban, Sifeta janar na ‘yan sanda, Usman Baba ya amince da nadin DSP Josephine Adeh a matsayin jami’ar hulda da jama’an rundunar ‘yan sanda na babban birnin tarayya, Abuja.
Daily Nigerian ta ruwaito cewa, a wata takarda wacce ya saki a ranar Talata a Abuja, ya ce sabuwar jami’ar hulda da jama’ar za ta fara aiki ne take-yanke.
Adeh ta maye gurbin ASP Daniel Ndirpaya ne wanda yanzu aka yi wa karin girma zuwa kwamishinan ‘yan sanda na Abuja a ranar 31 ga watan Augusta.
Asali: Legit.ng