Nnamdi Kanu ya maka kasar Kenya a kotu bisa laifin mika shi ga Najeriya

Nnamdi Kanu ya maka kasar Kenya a kotu bisa laifin mika shi ga Najeriya

  • Nnamdi Kanu ya maka gwamnatin kasar Kenya a kotu bisa laifin mika shi ga gwamnatin Najeriya
  • Takardar karar ta ce, shi Nnamdi Kanu tuni ya yi watsi da takardun zama dan Najeriya, yanzu shi dan Burtaniya ne
  • Takardar ta ambaci wasu jami'an gwamnatin kasar Kenya da Kanu yake kara a gaban wata kotu

Jagoran masu fafutukar kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu, ya maka Kenya a kotu saboda mika shi ga gwamnatin Najeriya, Punch ta ruwaito.

Dan uwansa, Kingsley Kanunta ne ya shigar da kara a madadinsa, kamar yadda takardun kotu suka nuna.

A cikin korafin da gungun lauyoyin Luchiri suka gabatar, Kanu ya bayar da hujjar cewa kamun da aka yi masa a Kenya da kuma mika shi ga Najeriya a watan Yuni ya sabawa tsarin mulki.

Kara karanta wannan

'Yan Majalisa na Kudu sun yi taro a gidan Ekweremadu kan ceto Nnamdi Kanu

Wadanda aka bayyana sunayensu a matsayin wadanda ake kara sune CS na cikin gida na Kenya, Daraktan Shige da Fice, Daraktan Binciken Laifuka, filin jirgin saman kasa da kasa na OCPD Jomo Kenyatta da Babban Lauyan Kasar ta Kenya.

Nnamdi Kanu ya maka kasar Kenya a kotu bisa laifin mika shi ga Najeriya
Shugaban IPOB, Nnamdi Kanu | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jami’an Najeriya a ranar 29 ga watan Yuni sun yi ikirarin cewa an dawo da Kanu Najeriya don fuskantar shari’a bayan da ya tsallake beli ya gudu a shekarar 2017.

Takardar ta bayyana cewa Kanu ya je Kenya ne don ganawa da likita bisa ciwon bugun zuciya da ke damunsa da kuma harkokin kungiyarsa ta IPOB.

A yayin da ake zargin mika Kanu ga Najeriya ba bisa ka'ida ba, karar ta ce:

“Batun (Kanu) dan Burtaniya ne mazaunin Ingila.
"Ya taba zama dan Najeriya amma ya yi watsi da hakan a 2015. Sakamakon haka hukumomin Najeriya suka kwace masa fasfo dinsa na Najeriya."

Kara karanta wannan

Binciko Gaskiya: Da gaske ne DSS sun kama telan Buhari da ya yi masa dinkin Imo?

Manya daga yankin kudu maso gabas sun kuduri kare Kanu

Sanatocin daga yankin kudu maso gabas a ranar Laraba, 15 ga watan Satumba, sun dauki matakin shiri don kafa kwamitin da zai binciki lamarin Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar IPOB domin a samu damar sakinsa.

Shirin, a cewar The Sun, shine tattaunawa da hukumomin gwamnatin tarayya da suka dace kan ci gaba da tsare Kanu.

Wadanda ke cikin wannan matakin sun hadu a gidan tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu a babban birnin tarayya Abuja.

Jiga-jigan na kabilar Igbo sun ce makasudin tsoma baki cikin aikin hukumomin shine don nemo mafita ta siyasa kan lamarin, in ji Premium Times.

Kakakin majalisa ya musanta kwatanta IPOB, 'yan Yarbawa da Boko Haram

A wani labarin, Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila ya yi watsi da wasu rahotannin da kafafen yada labarai ke yadawa da ke cewa 'yan arewan IPOB da Yarbawa duk daya ne da Boko Haram da ISWAP.

Kara karanta wannan

Jama’ar gari sun kashe wani da ake zargin dan fashi ne a Katsina

Lanre Lasisi, mai magana da yawun Gbajabiamila, ya yi karin haske a cikin wata sanarwa da aka aike wa Legit.ng a daren Laraba, 15 ga Satumba.

Ya bayyana cewa:

“Babu inda Shugaban Majalisar ya ambaci sunan wata kungiya. Abin da ya fito fili a cikin jawabin Shugaban Majalisar shi ne mayar da hankali kan ayyukan miyagun mutane da masu aikata laifuka, da tasirin su ga kasar.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel