Jama’ar gari sun kashe wani da ake zargin dan fashi ne a Katsina
- Wani da ake zargin dan bindiga ne ya gamu da ajalinsa a hannun mutanen gari a jihar Katsina
- Mutanen garin Magama da ke Karamar Hukumar Jibiya ta Jihar sun damke dan fashin tare da yi masa dukan kawo gishiri a yayin da ya ke siyan kwayoyi
- Sai daga baya ’yan banga suka kwace shi suka mika shi ga sojojin da ke sintiri a garin
Jibia, Katsina - Rahotanni sun bayyana cewa mazauna garin Magama a karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina sun yi nasarar kama wani mutum da ake zargi dan fashi ne.
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa dan fashin, wanda aka bayyana sunansa a matsayin Baleri, ya badda kamanni don siyan wasu magunguna a cikin garin.
Sai dai kuma, wasu mazauna garin sun gane shi sannan kuma suka far masa, amma a karshe kungiyar 'yan banga ta cece shi inda aka ce sun mika shi ga sojojin da ke sintiri a yankin.
Daga baya an ce an ga gawarsa a kusa da kauyen Kukar Babangida na karamar hukumar guda, amma babu cikakkun bayanai kan yadda a karshe ya mutu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jaridar Aminiya ta kuma ruwaito cewa jami'an 'yan sanda sun cafke 'yan uwansa guda uku da suka zo daukar gawarsa don yi masa jana'iza.
Wannan na zuwa ne yayin da aka dakatar da sabis na wayar sadarwa a wasu kananan hukumomin jihar, ciki har da Jibia.
Sauran kananan hukumomin da ke fama da matsalar rashin sabis sun hada da Faskari, Dandume, Funtua, Malumfashi, Bakori, Dutsin-Ma da Barsari da sauransu.
'Yan bindiga sun harbe 'yan sanda 3, sun kona gawarsu a Delta
A wani labarin na daban, mun ji cewa tashin hankali ya mamaye garin Umutu, a ƙaramar hukumar Ukwuani ta jihar Delta, bayan kisan wasu jami'an 'yan sanda uku na hedikwatar rundunar da ke garin.
Jaridar PM New ta ruwaito cewa wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba, ne suka kashe su da misalin karfe 7.40 na safiyar Laraba a wani shingen binciken ababen hawa da jami’an suka sanya a kan titin Obeti / Oliogo.
Majiyoyin yankin sun shaida wa jaridar cewa 'yan bindigar sun kuma kona motar sintiri kirar Toyota Sienna da aka ba sashen 'yan sanda na Umutu kwanan nan.
Asali: Legit.ng