Binciko Gaskiya: Da gaske ne DSS sun kama telan Buhari da ya yi masa dinkin Imo?
Kafofin sada zumunta sun cika da martani daga 'yan Najeriya wadanda suka bayyana ra'ayoyin su kan shigar Shugaba Muhammadu Buhari yayin ziyarar aiki ta kwana daya da ya kai jihar Imo don kaddamar da wasu manyan ayyuka a ranar Alhamis, 9 ga watan Satumba.
Da'awar da ake yadawa
Yayin da mutane da yawa ke jin cewa suturar da shugaban kasa Buhari ta kabilar Igbo (Isiagu, wato riga mai alamar kan zaki) ba ta sha dinki mai kyau, wasu sun zarce har da cewa ya kamata hukumar DSS ta kama telan da ya dinka suturar.
Wani sashe na masu sharhi a yanar gizo har ma ya kai ga yin ikirarin cewa hukumar tsaro ta DSS ta bi telan ta kwamushe shi.
Har ma an samu wani Simon Ekpa, wanda ya bayyana cewa shi mutumin Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar IPOB ne, a cikin rahoton Daily Post ya yi gargadin cewa a tabbatar babu abin da zai faru ga telan da ya dinka suturar.
Yadda gaskiyar lamarin yake
Amma don kwantar da hankalin al'umma da kuma sanar dasu gaskiya, dole ne a binciko gaskiyar lamari game da hoton da ake yadawa tare da maganganun da ke tattare shi.
Na farko dai, ya kamata a bayyana balo-balo cewa hukumar DSS na magance laifukan da suka shafi tsaron kasa ne saboda haka, ba ta da wata alaka da irin wadannan kananan laifuka.
Haka kuma, hukumar ba ta yin kasa a gwiwa wajen sanar da kamun da jami'an ta suka yi a kowane yanki na Najeriya.
Tabbatar da gaskiya
Da yake tabbatar da wannan bayanin, wani kwararre kan harkar tsaro wanda ya zanta da Legit.ng bisa sharadin a sakaya sunansa a ranar Asabar, 11 ga Satumba, game da batun ya lura cewa jami'an DSS ba za su iya yin kasa a gwiwa ba ko saibi a cikin ayyukansu.
Ya bayyana cewa:
“Hukumar DSS ba ta da wata alaka da wani tela; mutumin da ya kamata a dora wa alhakin kuskuren (idan ma gaskiya ne) shi ne/su ne ke da alhakin kawo suturarsa.
"Shugaban yana da mashawarta da yawa a tare dashi, menene martaninsu na gaggawa lokacin da suka ga suturar?"
Hukuncin bincike kan batun
DSS ba ta kama wani telan da ya dinkawa shugaba Buhari suturar da ya je jihar da ita ba. Saboda haka, labarai ne na karya da ake yadawa da basu da hujja ko makama.
Mun yi ta yi wa Buhari addu’o'i amma ba mu ga sakamako ba, inji Sheikh Khalid
A wani labarin, Babban limamin masallacin Juma’a na Apo Legislative Quarters dake Abuja, Sheikh Muhammad Khalid, kwanan nan ya yi fice a kafafen sada zumunta bayan faifan bidiyon wa’azin sa da ya soki shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bazu.
A cikin wata hirar da Legit.ng Hausa ta samo daga jaridar Punch, malamin addinin Islaman ya ce yana tsaye kan kalamansa cewa shugaban bai tsinana komai ba.
A tattaunawar, malamin ya bayyana abubuwan da suke damunsa game da gwamnatin shugaba Buhari, wadanda a cewarsa gwamnatin ta cika yiwa 'yan Najeriya karerayi.
Asali: Legit.ng