Zamfara: 'Yan bindiga sun kai farmaki sansanin sojoji, jami'ai 12 sun tafi barzahu

Zamfara: 'Yan bindiga sun kai farmaki sansanin sojoji, jami'ai 12 sun tafi barzahu

  • 'Yan fashin daji sun kai farmaki sansanin sojoji da ka Mutumji a karamar hukumar Dansadau ta jihar Zamfara
  • Mummunan harin ya yi ajalin jami'ai 12 da suka hada da sojin sama 9, 'yan sanda 3 da sojan kasa 1 a take
  • Miyagun 'yan bindigan sun kwashe makamai da wasu kayan aikin sojin tare da banka wa wani sashin sansanin wuta

DanSadau, Zamfara - Miyagun 'yan bindiga a ranar Asabar sun kai farmaki sansanin sojoji a jihar Zamfara inda suka sheke zakakuran jami'ai 12 a take.

Kamar yadda wadanda suka ga aukuwar lamarin suka sanar da Premium Times, sun ce a kalla jami'ai 12 an tabbatar da mutuwarsu yayin da wasu uku suka raunata a yayin harin da aka kai musu a sansanin Mutumji da ke karamar hukumar Dansadau a jihar Zamfara.

Mummunan lamarin ya auku ne yayin da ake tsaka da tsananta matsantawa 'yan bindigan da suka addabi yankin arewa maso yammacin kasar nan.

Zamfara: 'Yan bindiga sun kai farmaki sansanin sojoji, jami'ai 12 sun tafi barzahu
Zamfara: 'Yan bindiga sun kai farmaki sansanin sojoji, jami'ai 12 sun tafi barzahu. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

An sheke 'yan bindiga masu tarin yawa yayin da aka damke wasu sakamakon ayyukan da sojoji suka tsananta wanda har ya kai ga an datse hanyoyin sadarwa a Zamfara da wasu bangarorin jihar Katsina.

Wannan farmakin da miyagun suka kai sansanin sojojin kamar yadda majiya ta tabbatar, ya bar sojojin sama tara, 'yan sanda biyu da sojan kasa daya babu rai, Premium Times ta ruwaito.

'Yan bindigan sun kara da yin awon gaba da makamai tare da wasu kayan aikin shekakkun jami'an yayin da suka banka wa wani sashi na sansanin wuta.

Har zuwa daren Lahadi, ba a samu mai magana da yawun ma'aikatan tsaro, Benjamin Sawyerr ba domin tsokaci.

Yadda sojoji suka yi wa direban tasi dukan fitar rai a Jos

A wani labari na daban, sojojin da ke aiki da Operation Safe Haven (OPSH), wata hukumar tsaron hadin guiwa da ke da alhakin samar da zaman lafiya a Plateau, a daren Juma'a, ana zarginsu da yi wa direban tasi mai suna Sadik Abdullahi Karafa dukan mutuwa.

Daily Trust ta ruwaito yadda ake zargin sojojin da yi masa dukan a kasuwar Paringada yayin da ya ke hanyar dawowa daga Mangu, sa'a daya kafin dokar ta bacin ta fara aiki.

Dokar ta bacin ta na aiki ne daga karfe goma na dare zuwa shida na safe amma Sadik ya dawo wurin karfe tara da minti ashirin na dare, Daily Trust ta wallafa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel