Yadda sojoji suka yi wa direban tasi dukan fitar rai a Jos

Yadda sojoji suka yi wa direban tasi dukan fitar rai a Jos

  • Ana zargin sojojin Operation Safe Haven (OPSH) da ke Jos da yi wa wani direban tasi dukan mutuwa
  • An gano cewa, ya isa wurin Faringada sa'a 1 kafin dokar ta-baci ta fara aiki amma sojojin suka tare shi tare da dukan shi
  • 'Yan uwan shi sun tsinci gawarsa a ranar Asabar, lamarin da yasa suka kai rahoto wurin 'yan sanda amma bayanin komai

Jos - Sojojin da ke aiki da Operation Safe Haven (OPSH), wata hukumar tsaron hadin guiwa da ke da alhakin samar da zaman lafiya a Plateau, a daren Juma'a, ana zarginsu da yi wa direban tasi mai suna Sadik Abdullahi Karafa dukan mutuwa.

Daily Trust ta ruwaito yadda ake zargin sojojin da yi masa dukan a kasuwar Paringada yayin da ya ke hanyar dawowa daga Mangu, sa'a daya kafin dokar ta bacin ta fara aiki.

Yadda sojoji suka yi wa direban tasi dukan fitar rai a Jos
Yadda sojoji suka yi wa direban tasi dukan fitar rai a Jos. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Dokar ta bacin ta na aiki ne daga karfe goma na dare zuwa shida na safe amma Sadik ya dawo wurin karfe tara da minti ashirin na dare, Daily Trust ta wallafa.

Abdullahi Karafa, wani babban yayan mamacin, ya bayyana cewa sojoji ne suka halaka kaninsa.

Ya ce:

"Mu na gida lokacin da wani abokinmu ya kira ni kan cewa sojoji sun kama kanina kuma suna dukan shi a wurin babban titin Faringada. Da jin haka, daya daga cikin kannanmu, Umar Abdullahi ya hanzarta zuwa wurin kuma ya samu sojojin suna dukan shi.
"Lokacin da ya sanar da su cewa Sadik dan uwan shi ne, sun yi banza da shi tare da saka shi a Hilux. Kaninmu ya dawo gida daren Juma'a kuma mun yanke hukuncin zuwa da safe. Da safiyar Asabar mu ka je Faringada inda muka tarar da gawar shi.

“Mun dauka gawar shi inda muka kai ta ofishin 'yan sandan Katako domin kai rahoton lamarin. Ba bu wani bayanin dalilin da yasa aka mishi mugun dukan. Kwamandan Div 3 ya kawo mana ziyara tare da alkawarin cewa za a tabbatar da an yi adalci. Ba za mu bar wannan abun ba, muna neman adalci," ya kara da cewa.

A yayin da aka tuntubi mai magana da yawun OPSH, Ishaku Takwa, ya ce zai bincika kuma zai kira mu, amma har yanzu shiru.

Marwa: NDLEA ta kwace miyagun kwayoyi na N6bn masu alaka da ISIS

A wani labari na daban, shugaban hukumar yaki da safarar miyagun kwayoyi ta NDLEA, Buba Marwa, ya bayyana yadda suka kwace miyagun kwayoyi masu kimar naira biliyan 6 a filin jirgin ruwa da ke Apapa, jihar Legas.

TheCable ta ruwaito cewa, ya yi wannan jawabin ne a ranar Laraba inda shugaban NDLEA din ya ce kwayoyin sun zo ne daga gabas ta tsakiya.

A cewarsa, hukumar ta samu bayanan sirri ne daga abokan huldar ta dangane da safarar kwayoyi ta filin jirgin Apapa. Marwa ya ce kwayoyin masu suna Captagon suna da alaka da kungiyar ‘yan ta’adda da ke gabas ta tsakiya, TheCable ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Tags:
Jos
Online view pixel