Kungiyar Miyetti Allah ta nisanta kan ta daga furucin da sakatarenta ya yi a kan Masari

Kungiyar Miyetti Allah ta nisanta kan ta daga furucin da sakatarenta ya yi a kan Masari

  • Miyetti Allah nisanta kan ta daga furucin sakatarenta, Saleh Alhassan da ya yi akan gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, inda ya kira shi da dan giya kuma gajiyayyen shugaba
  • Rahotanni sun nuna yadda gwamna Masari ya fito karara ya bayyana cewa yawancin ‘yan bindiga Fulani ne, wanda hakan ya hassala sakataren kungiyar har ya yi furucin akan sa
  • A ranar Juma’a shugaban kungiyar na reshen jihar Katsina, Hassan Kuraye ya ce kungiyar ba ta da alaka da furucin Alhassan, sannan bai nemi izinin kungiyar ba kafin ayi hirar da yayi furucin ba

Jihar Katsina - Kungiyar makiyaya Fulani ta Miyetti Allah ta nuna rashin amincewar ta da furucin da sakataren ta na kasa ya yi akan gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari inda ta kira shi da dan giya, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kai Ɗan Kanzagi Ne, Muƙunshin Gishiri Ka Fi Gishiri Zaƙi, Gumi Ya Yi Wa Kakakin Buhari Wankin Babban Bargo

Rahotanni sun nuna yadda Masari ya bayyana yana cewa yawancin ‘yan bindiga Fulani ne, furucin da ya tunzura Alhassan har ya caccaki gwamnan.

Kungiyar Miyetti Allah ta nisanta kan ta daga furucin da sakatarenta ya yi a kan Masari
Gwamna Aminu Bello Masari na Jihar Katsina. Hoto: Premium Times
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugabannin kungiyar na reshen jihar Karsina sun nisanta kansu daga furucin Saleh Alhassan.

Kamar yadda Premium Times ta ruwaito, Alhassan ya furta munanan kalaman ga gwamnan ne saboda haushin cewa da ya yi yawancin ‘yan bindiga Fulani ne.

Furucin da Masari ya yi har Saleh Alhassan ya kira shi da dan giya

A wata hira da aka yi da Gwamna Masari a Channels TV ya ce:

“Akwai mutane iri na da suke irin yare na har da irin addini na a cikin su,”
“Don haka anan akwai ‘yan bindiga; ba wasu halittu bane na daban, mutane ne da muka sani kuma sun dade su na rayuwa tare da mu tsawon shekaru 100 ma.”

Kara karanta wannan

Buhari: Gwamnan Ebonyi ya yi wa Wike raddi, ya fallasa wadanda suka kawo matsalar tsaro

Shugaban Miyetti Allah na jihar Katsina ya ce sakataren ba ra’ayin kungiyar ya fadi ba

Sai dai kamar yadda Premuim Times ta ruwaito, a wata tattaunawa da manema labarai su ka yi da Hassan Kuraye, shugaban kungiyar na jihar Katsina, Alhassan ya fadi son ran sa ne kuma bai nemi izini ba kafin ayi hirar da shi

A cewarsa:

“Munyi magana da shugabannin kungiyar Miyetti Allah na kasa sun ce Alhassan bai bayyana matsayar kungiyar ba dangane da lamarin”

Yayin bayyana ra’ayin sa dangane da furucin Masari, Kuraye ya bayar da hakuri a madadin kungiyar ga Masari inda ya bukaci ya yafe musu kuma ya manta da maganganun da sakataren su ya yi akan sa.

Ya ce shugaban kungiyar zai tattaro sauran masu ruwa da tsakin kungiyar a mako mai zuwa don su yi magana da gwamna akan lamarin.

Masari: Mafi Yawancin Ƴan Bindiga Fulani Ne Da Ke Cewa Su Musulmi Ne Kaman Ni

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Jami'in dan sanda ya harbe abokin aikinsa dan sanda a jihar Kano

Tunda farko, Legit.ng ta kawo muku cewa Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina ya ce mafi yawancin 'yan bindiga fulani ne kaman shi, ya kara da cewa suna magana harshen Fulfulde kuma suna cewa su musulmi ne, The Punch ta ruwaito.

Ya ce mafi yawancin yan arewa ba su za su yarda da hakan ba amma ya ce zancensa gaskiya ne

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya ke magana a shirin siyasa na 'Politics Today' a gidan talabijin na Channels.

Asali: Legit.ng

Online view pixel