Buhari: Gwamnan Ebonyi ya yi wa Wike raddi, ya fallasa wadanda suka kawo matsalar tsaro

Buhari: Gwamnan Ebonyi ya yi wa Wike raddi, ya fallasa wadanda suka kawo matsalar tsaro

  • Dave Umahi yana nan a kan bakarsa na rokon Ubangiji ya kawo wa wani irin Buhari
  • Wannan magana da gwamnan Ebonyin ya yi, ya jawo masa raddi daga Nyesom Wike
  • Kwamishinan labaran jihar Ebonyi ya kare gwamnan, ya yabawa gwamnatin Buhari

Abakaliki - Kwamishinan harkokin yada labarai da wayar da kan al’umma na jihar Ebonyi, Orji Uchenna Orji, ya jaddada maganar da David Umahi yayi.

Barista Orji Uchenna Orji yace Mai girma gwamnan Ebonyi, David Umahi bai yi nadamar kalaman da ya yi a game da samun irin Muhammadu Buhari a 2023 ba.

Daily Trust tace Uchenna Orji ya shaida wa manema labarai cewa ganin yadda Buhari yake shawo kan matsalar tsaro, shiyasa yace a roki wani irinsa.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Wuta ‘yan bindiga za su, fadar Shugaban kasa ta mayar da martani ga Sheikh Gumi

“Saboda haka ina tunanin ta ko ina, Gwamna Dave Umahi yayi daidai, saboda idan ka duba kiraye-kirayen da ake yi na addini da kabilanci, da a ce ba mutum mai dattaku irin Buhari ba ne, da abubuwan sun fi haka muni.”
“Kafin ya hau mulki, ‘yan bindiga sun cika babban birni, amma da ya shiga ofis, mun daina jin labarin ta’adin wadannan ‘yan bindiga a Birane, saboda haka ya yi kokari.”

Kwamishinan yada labaran yake cewa gwamnatin Muhammadu Buhari ta kawo tsare-tsaren taimaka wa marasa galihu a karkashin babban banki na CBN.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnan Ebonyi
Gwamnan Ebonyi, Umahi Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Sannan a cewar Uchenna Orji, shugaban Najeriyar ya tafi da kowane bangare na kasar nan a mulkinsa.

Jaridar ta rahoto Kwamishinan yana bayani game da ziyarar da Buhari ya kai Imo, yace mutane sun zauna a gida ne saboda tsoro ba don yi wa IPOB ladabi ba.

Kara karanta wannan

Zan taimakawa jihar Imo wajen magance matsalar tsaro, Shugaba Buhari

Su wanene suka jawo matsalar tsaro?

“Sha’anin rashin tsaro ba matsalar gwamnatin nan mai-ci ba ce, gwamnatin baya da wasu masu ruwa-da-tsaki a gwamnatin nan suka kawo ta.”
“Ba na cikin gwamnati kadai ba, har da wadanda ba su cikin masu rike da madafan iko.”

Tun ba yau ba ake kashe mutane a Zamfara

Wani Masani a jami'ar UDUS, Dr. Murtala A. Rufa’i, da ya dade yana binciken rikicin Zamfara ya gabatar da takarda a yauJuma'a inda ya dauko nasabar sha'anin.

Dr. Rufa’i wanda ya yi shekara da shekaru yana nazarin lamarin jihar Zamfara, yace tun kafin turawan mulkin mallaka suka zo ake kashe mutane a Zamfaran.

Asali: Legit.ng

Online view pixel