Kai Ɗan Kanzagi Ne, Muƙunshin Gishiri Ka Fi Gishiri Zaƙi, Gumi Ya Yi Wa Kakakin Buhari Wankin Babban Bargo

Kai Ɗan Kanzagi Ne, Muƙunshin Gishiri Ka Fi Gishiri Zaƙi, Gumi Ya Yi Wa Kakakin Buhari Wankin Babban Bargo

  • Gumi ya mayar da martani mai zafi ga kakakin shugaban kasa, Femi Adesina kan ya kira shi da masoyin ‘yan ta’adda
  • Sheikh Gumi ya ce Adesina makunshin gishiri ne da har zai kira shi da masoyin ‘yan bindiga
  • A cewar Gumi shi masoyin kasar sa ne, yankin sa, jihar sa, mutanen sa da duk wasu bil’adama

Wasa-wasa Sheikh Ahmed Gumi ya soka wa kakakin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Femi Adesina maganganu masu zafi, inda ya ce 'sakarai ne kadai zai bari yankinsa ya zama filin daga', kamar yadda News Wire NGR ta ruwaito.

A cikin wata wallafa da ya yi a baya-bayan nan, Adesina wanda ya ce 'babu inda yan bindiga zasu' ya yabawa sojoji bisa ragargazan da suke yi wa 'yan bindiga a arewa maso yamma kuma ya yi ikirarin cewa mai son 'yan bindigan ya fito yana ta kwakwazo.

Kara karanta wannan

Gyadar doguwa: Yadda ya tsira daga hannun Miyagun da suka yi garkuwa da shi - Gumi

Kai Ɗan Kanzagi Ne, Muƙunshin Gishiri Ka Fi Gishiri Zaƙi, Gumi Ya Yi Wa Kakakin Buhari Wankin Babban Bargo
Sheikh Ahmad Gumi da Femi Adesina. Hoto: LIB
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai bayan ganin wannan wallafar, Sheikh Gumi ya mayar da martani ta shafinsa na Facebook inda ce:

“Kai makunshin gishirin da ya kira ni da masoyan ‘yan bindiga! Ba haka nake ba, ni masoyin yanki na ne, kasa ta, jiha ta, mutane na da sauran bil’adama.”

Sheikh Gumi ya dade yana kira ga gwamnati ta yi wa 'yan bindiga afuwa

Sau da yawa Gumi ya sha nuna rashin amincewar sa akan yadda gwamnatin tarayya take ragargazar ‘yan bindiga

Malamin ya ce wajibi ne a yafe wa ‘yan bindiga kuma Najeriya ta basu dama don a kawo karshen ta’addanci.

Ya nuna rashin amincewar sa akan cigaba da yaki da zubar da jini inda ya ce indai har ana iya yefe wa masu manyan laifuka, lallai ya kamata a yafe wa ‘yan bindiga.

Kara karanta wannan

Ni Soja ne, Likita kuma Malami mai Digiri 3, saboda haka ba zan yi shiru ba: Sheikh Gumi

Kamar yadda ya ce:

“Ni cikakken likita ne, likitan da ya san yadda zai yi aiki a kwakwalwa ba tare da lalata bangarori masu hatsari ba a cikin ta.
“Ni soja ne, wanda ya san aikin sojoji da karfin sojojin mu.
“Ina da digiri 3 kuma duka daga kasar waje na samo su. Ni malamin musulunci ne wanda yasan illar hallaka rayukan da basu ji ba basu gani ba. Don haka bai dace in yi shiru ba.
“Sakarai ne kadai zai bari yankin sa ya koma filin daga, sai dai kash! akwai sakarkaru da dama.
“Hallaka beraye a mazaunin ka da sandar karfe zai iya janyo kayi asarar abubuwan ka masu muhimmanci da daraja kila kuma ba za ka samu damar hallaka ko daya ba.”

Sheikh Gumi ya faɗawa Fulani yadda za su yi wa kansu gata a Nigeria

A wani labarin daban, Malamin addinin musulunci mazaunin Kaduna, Dr Ahmad Gumi, ya yi kira ga fulani a su tabbatar sun yi rajista sun kuma karbi katin zabe gabanin babban zaben 2023 da ke tafe a kasar, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Wuta ‘yan bindiga za su, fadar Shugaban kasa ta mayar da martani ga Sheikh Gumi

A cewarsa, samun katin zaben yana da muhimmanci domin hakan zai basu damar zaben shugabanni da za su yi jagoranci na gari sannan su kare musu hakkokinsu.

Gumi ya ce akwai bukatar Fulani su yi rajistan kamar sauran yan Nigeria, domin su zabi mutanen da za su kiyayye musu dabobinsu da dukiyoyinsu da rayukansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel