Masari: Mafi Yawancin Ƴan Bindiga Fulani Ne Da Ke Cewa Su Musulmi Ne Kaman Ni

Masari: Mafi Yawancin Ƴan Bindiga Fulani Ne Da Ke Cewa Su Musulmi Ne Kaman Ni

  • Gwamna Aminu Masari ya ce mafi yawancin 'yan bindigan da ke arewa maso yamma Fulani ne
  • Gwamnan na jihar Katsina ya kuma ce 'yan bindigan da ke yankin arewa galibinsu musulmi ne kamar shi
  • Gwamna Masari ya ce 'yan arewa da dama ba za su yarda da abin da ya fada ba amma zancensa gaskiya ne

Jihar Katsina - Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina ya ce mafi yawancin 'yan bindiga fulani ne kaman shi, ya kara da cewa suna magana harshen Fulfulde kuma suna cewa su musulmi ne, The Punch ta ruwaito.

Ya ce mafi yawancin yan arewa ba su za su yarda da hakan ba amma ya ce zancensa gaskiya ne.

Masari: Mafi Yawancin Ƴan Bindiga Fulani Ne Da Ke Cewa Su Musulmi Ne Kaman Ni
Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari. Hoto: The Punch
Asali: Twitter

Kara karanta wannan

'Yan Bindigan Zamfara Na Neman Fushin Allah Ya Sauka a Kansu, Sheikh Abdullahi Dalla-Dalla

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya ke magana a shirin siyasa na 'Politics Today' a gidan talabijin na Channels.

Kalamansa:

"Mutane ne kaman ni, wadanda ke magana da harshe irin nawa, kuma su na cewa suna addini irin nawa.
"Don haka abin da muke fama da shi shine 'yan bindiga; ba baki bane daga wani duniyan, mutane ne da suke zama da mu na daruruwan shekaru.
"Masu shigowa daga kasashen Afirka ta Yamma da Afirka ta Arewa suma Fulani ne.
"Mafi yawancin 'yan bindihga da ke addabar mu Fulani ne, ko da yana da dadin ji ko ba shi da dadin ji amma dai wannan shine gaskiya. Ba cewa na ke yi dukkan Fulani ne ba amma galibinsu fulani ne, kuma wadannan mutane ne da ke zaune a daji kuma babban sana'arsu shine kiwon dabobi."

Ya kara da cewa akwai kimanin kungiyoyi 100 da suka hada da 'yan fashin daji, masu garkuwa, masu fyade da masu fashi da makami.

Kara karanta wannan

Bagudu: Muguntar 'yan bindiga ta fi shafar Fulani, ba mu sauraron labaransu ne kawai

'Yan Bindigan Zamfara Na Neman Fushin Allah Ya Sauka a Kansu, Sheikh Abdullahi Dalla-Dalla

A wani labarin daban, Babban limamin masallacin Juma'a na Sambo Dan-Ashafa da ke Gusau, Sheikh Abdullahi Dalla-Dalla, a ranar Juma'a ya gargadi 'yan bindigan da ke jihar su janye ko su gamu da fushin Allah, Daily Nigerian ta ruwaito.

A yayin hudumar Juma'a da ya yi, ya ce kashe mutane da keta hakkinsu a jihar zai haifar da fushin Allah, idan har masu aikata laifin ba su tuba sun dena ba kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Dalla-Dalla ya ce:

"Abin da na ke kira ga 'yan bindigan shine su tuba; su dena kashe mutanen da ba-su-ji-ba-ba su gani ba sannan su mika mukamansu kafin fushin Allah ya sauka a kansu."

Asali: Legit.ng

Online view pixel