Sultan: Allah bai yi kuskure ba da ya haɗa mu zama tare a matsayin ƴan Nigeria

Sultan: Allah bai yi kuskure ba da ya haɗa mu zama tare a matsayin ƴan Nigeria

  • Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar ya yi kira ga yan Nigeria su so juna su kuma hada kai
  • Sultan din ya yi wannan kiran ne a wurin wani taro a Abuja yana mai cewa Allah bai yi kuskure ba da ya hada mu zama tare
  • Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar ya yi zargin wasu na neman amfani da addini don raba kasar amma ya ce ba za suyi nasara ba

Abuja - Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa'ad Abubakar na III, ya bukaci dukkan kabilun Nigeria su cigaba da zama a matsayin yan uwan juna domin Allah bai yi kuskure ba da ya hada mu zama a matsayin kasa daya, Daily Trust ta ruwaito.

Da ya ke jawabi a matsayinsa na shugaba a wurin taron bada lambar yabo na shugabanci na 2020 a ranr Alhamis a Abuja, Sultan ya ce raba kasar ba zai magance matsalolin da kowace kabilar ke fama da shi ba amma hada kai tare a warware matsalar ce ta fi amfani.

Kara karanta wannan

Buhari yace yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya yana da matukar wahala

Sultan: Allah bai yi kuskure ba da ya haɗa mu zama tare a matsayin ƴan Nigeria
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sultan din ya ce:

"Idan muka rabu kowa ya kama gabansa, ta yaya za mu rayu? Allah bai taba kuskure ba kuma baya kuskure, wannan shine kaddararsa kuma ya kamata mu rungume kadarar.
"Hada mu a matsayin yan Nigeria ba kuskure bane kuma wannan shine abin da Allah ya so. Idan yana son wani abin daban da tuni ya yi don haka ya kamata mu rungumi addinan mu a matsayin musulmi da kirista.
"Dukkanmu mun san daga mahallici daya muke."

Sultan ya ce wadanda ke amfani da addini domin raba kan mutane ba za su yi nasara ba domin mutanen kasar ba za su biye musu ba.

Ya kuma shawarci yan Nigeria su bada gudumawarsu don ganin an samar da tsaro a kasar.

Abin da Osinbajo ya ce wurin taron?

Kara karanta wannan

Masari: Mafi Yawancin Ƴan Bindiga Fulani Ne Da Ke Cewa Su Musulmi Ne Kaman Ni

A jawabinsa, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya ce bai amince da batun da wasu ke yi ba na cewa hada mu da turawan mulkin mallaka suka yi ya hana kasar cigaba kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce tarihi ya nuna cewa yankunan suna huldar kasuwanci da juna don haka ba baki bane. Amma ya ce akwai laifin shugabanni da suka gaza gina hukumomi da za su kula da al'umma.

Sheikh Gumi ya faɗawa Fulani yadda za su yi wa kansu gata a Nigeria

A wani labarin daban, Malamin addinin musulunci mazaunin Kaduna, Dr Ahmad Gumi, ya yi kira ga fulani a su tabbatar sun yi rajista sun kuma karbi katin zabe gabanin babban zaben 2023 da ke tafe a kasar, Daily Trust ta ruwaito.

A cewarsa, samun katin zaben yana da muhimmanci domin hakan zai basu damar zaben shugabanni da za su yi jagoranci na gari sannan su kare musu hakkokinsu.

Kara karanta wannan

Dalilin da ya sa Buhari ya miƙa min ma'aikatar lantarki, Sabon Minista, Aliyu

Gumi ya ce akwai bukatar Fulani su yi rajistan kamar sauran yan Nigeria, domin su zabi mutanen da za su kiyayye musu dabobinsu da dukiyoyinsu da rayukansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel