Dalilin da ya sa Buhari ya miƙa min ma'aikatar lantarki, Sabon Minista, Aliyu
- Abubakar Aliyu, sabon ministan lantarki ya ce ba hakanan kawai Shugaba Buhari ya nada shi ministan makamashi ba
- Aliyu ya bayyana cewa shugaban kasar ya nada shi ministan ne domin ya tafi ya tabbatar komai ya tafi dai-dai a ma'aikatar kuma an ci nasara
- Ministan ya bayyana hakan ne yayin jawabinsa da ya yi a lokacin da ya ke ganawa da direktoci da ma'aikatan ma'aikatar na lantarki
FCT, Abuja -Sabon Ministan Lantarki, Injiniya Abubakar Aliyu, ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya tura shi ya karbi ragamar shugabanci a ma'aikatar ne saboda wani dalili na musamman, Daily Trust ta ruwaito.
Daily Trust ta ruwaito cewa Aliyu ya bayyana hakan ne yayin da ya kama aiki a Ma'aikatar Makamashi a Abuja a ranar Litinin.
Da ya ke yi wa direktoci da ma'aikatan ma'aikatar jawabi, ya ce:
"Na san kun yi aiki sosai, Na zo nan ne domin in taimaka muku, ko da ba ku ko babu ku domin abin da aka turo ni in tabbatar shine mu yi nasara. Wanda ya dauke ni aiki ya turo ni nan ne saboda wani dalili."
Da ya ke bayyana dalilin, Sabon Ministan Makamashin ya ce an turo shi ne domin ya tabbatar an yi komai yadda ya dace a bangaren makamashi.
Aliyu ya kuma nemi hadin kan masu ruwa da tsaki yana cewa;
"Ba hanayenku kadai na ke so ba wurin aiki har da zuciyarku. nan ne gaskiya da jajircewa ya ke.
"Aikin mu zai taba rayukan dukkan yan Nigeria don haka a zo nan ne domin in kara wa aikin ku inganci."
Ministan yayin da ya ke neman goyon bayan jami'an ma'aikatan ya ce ya saurari mukaman jami'an amma yana bukatar hakan ya zama aiki.
Martanin sakataren dindindin na ma'aikatar makamashi
Sakataren dindindin na ma'aikatar, Mr Williams Alo ya ce jami'an a shirye suka su bawa ministan goyon bayan da ya ke bukata.
Alo ya ce:
"Mun san ka zo nan ne domin ka cigaba da aiki mai kyau na shugaban kasa da ya shafi sashin makamashi. Muna tabbatar da maka cewa za mu mayar da hankali don yin ayyukan mu."
Sale Mamman: Abin da yasa ban koma gidana ba tun bayan da Buhari ya kore ni
A wani labarin daban, Sale Mamman, tsohon ministan makamashi, ya yi bayanin abin da yasa bai koma gidansa ba bayan shugaba Muhammadu Buhari ya sallame shi daga aiki, rahoton Daily Trust.
Wasu rahotanni sun ce an kwantar da ministan a asibiti bayan ya samu labarin cewa an kore shi.
Amma, a wata hirar wayar tarho da ya yi da BBC Hausa, Mamman ya karyata rahoton.
Asali: Legit.ng