‘Dan wasan Argentina, Messi ya rusa tarihin Pele, amma har yanzu yana bayan Cristiano Ronaldo

‘Dan wasan Argentina, Messi ya rusa tarihin Pele, amma har yanzu yana bayan Cristiano Ronaldo

  • Lionel Messi ya ci kwallayensa na 77, 78 da 79 a wasansu da kasar Bolivia
  • Tauraron shi ne ‘dan kwallon Kudancin Amurkan da ya fi kowa kwallaye
  • ‘Dan wasan na Argentina ya sha gaban Pele, amma Ronaldo na gaba da shi

Argentina - Lionel Messi ya zarce kowa a matsayin ‘dan wasan kwallon kafan nahiyar Amurka ta kudu da ya fi kowa yawan kwallaye a tarihin Duniya.

BBC ta kawo rahoto cewa Lionel Messi ya rubuta sunansa a littafin tarihi bayan ya jagoranci kasarsa ta Argentina zuwa ga nasara a wasan Bolivia.

Sabon ‘dan wasan gaban kungiyar PSG, ne ya zura kwallaye uku a wasan da aka buga a Buenos Aires. Haka ya sa adadin kwallayensa a gida suka kai 79.

Messi ya yi wa Pele gaba

Kara karanta wannan

Jerin manyan jami'an gwamnati 5 da shugaba Buhari ya kora cikin kankanin lokaci

Da kwallaye 79 a wasanni 153, Messi ya sha gaban Pele wanda shi ne ke rike da wannan tarihi kafin wasan da aka buga a ranar 9 ga watan Satumba, 2021.

A lokacin da Pele yake buga wa kasar Brazil wasa, ya zura kwallaye 77 a cikin wasanni 92. Pele ya sa wa kasarsa riga ne daga shekarar 1956 zuwa 1970.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Messi ya fara ne da bugun finariti a minti na 14, sai ya sake cin kwallo da aka dawo hutun rabin lokaci. Ana daf da za a tashi, ‘dan wasan ya ci ta ukunsa.

Messi v Bolivia
Messi ya na wasa a Argentina Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Duniya ta yi wa Messi dadi

Rahoton yace bayan an tashi wasan, ‘yan wasan Argentina sun fito da kofin gasar Copa Amurka da suka lashe a Yuli domin na filin kwallon su shaida.

Kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Instagram, Messi ya yi murnar samun wannan nasara a tarihi. Tauraron yace ya taba mafarkin irin wannan rana.

Kara karanta wannan

Likitoci sun fede wani mutum, sun ciro Nokia 3310 da ya hadiye

“Ban san yadda zan gode maku da soyayyar da kuka nuna mani ba. Na ji dadi, ba zan taba manta wa ba.”

‘Yan wasan matan kasar Brazil, Marta mai kwallaye 109 da kuma Cristiane mai kwallaye 96 ne kadai ‘yan kwallon nahiyar da suka sha gaban Lionel Messi.

Ya ratar Messi da Ronaldo a gida?

Kuna da labari a duk Duniya babu ‘dan wasan da yake da yawan kwallaye a kasarsa irin Cristiano Ronaldo bayan ya ci kwallo biyu a wasansu da Ireland.

Ronaldo ya shiga littafin tarihi, ya ci wa kasar Portugal kwallaye 111. Hakan yana nufin akwai tazarar kwallaye 32 tsakaninsa ‘dan wasan na Argentina.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng