Cristiano Ronaldo ya kafa sabon tarihi da kasar Portugal a Duniyar wasan kwallon kafa

Cristiano Ronaldo ya kafa sabon tarihi da kasar Portugal a Duniyar wasan kwallon kafa

  • Cristiano Ronaldo ya zura kwallaye biyu a wasan Portugal da Ireland
  • Hakan yana nufin Ronaldo ya ci kwallaye har 111, fiye da kowa a tarihi
  • Tsohon ‘dan wasan Juvenuts shi ne ‘dan wasan da ya fi kwallaye a gida

Portugal - Cristiano Ronaldo mai Ballon d'Or biyar, ya sake kafa sabon tarihi a kwallon kafa, inda ya ci wa Portugal kwallaye a wasansu da Ireland.

Goal.com ta rahoto cewa ‘dan wasan gaba, Cristiano Ronaldo ya shiga littafin tarihi ne yayin da ya ci wa kasar Portugal kwallayensa na 110 da 111.

A ranar 1 ga watan Satumba, 2021, Ronaldo ya zarce Ali Daei a yawan kwallayen da aka ci wa kasa.

Ronaldo ya ceci Portugal a filin wasa na Estadio Algarve a minti na 89. Ana shirin tashi ne kuma ‘dan kwallon ya sake jefa kwallo a ragar Ireland.

Kara karanta wannan

Shekaru 35 yana aikin koyarwa a Borno, dan Najeriyan da Turawa suka horar ya koma talla

Da wadannan kwallaye da sabon ‘dan wasan na Manchester United ya ci, ya ba Portugal nasara a kokarin zuwa gasar kofin Duniya da za ayi a 2022.

BBC ta ce Ronaldo mai shekara 36 ya na da kwallaye 111 a kasar Portugal, ba a taba samun ‘dan wasan da yake da yawan wadannan kwallaye ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Cristiano Ronaldo
Cristiano Ronaldo vs Ireland Hoto: www.dailymail.co.uk
Asali: UGC

Yadda Ronaldo ya ajiye tarihi

A wasan Portugal da Faransa a gasar Euro 2020 ne Ronaldo ya kamo Ali Daei wanda ya taba ci wa Iran kwallaye 109 a lokacin da yake buga kwallo.

Goal ta ce da wadannan kwallaye Ronaldo ya sha gaban Miroslav Klose a matsayin ‘dan wwasan Turan da ya fi kowa yawan kwallaye a wannan mataki.

Bugu da kari, Ronaldo ne kadai ‘dan wasan da ya taba zura kwallaye a gasar Euro biyar a jere.

Kara karanta wannan

NDA: Babban malamin adddini ya aika gagarumin gargadi ga 'yan Najeriya, ya ce karin matsaloli na tafe

Su wanene suka fi yawan kwallaye da rigar kasarsu?

1. Cristiano Ronaldo (111)

2. Ali Daei (109)

3. Puskas (84)

4. Kamamoto (80)

5. Chitalu (79)

Ronaldo zai tashi da kudi jaba-jaba a Ingila

Kuna da labari za a rika biyan Cristiano Ronaldo £480,000 a kowane mako. Hakan na nufin duk Ingila babu ‘dan wasan da zai rika karbar albashi kamarsa.

Ronaldo ya sha gaban Tauraron Manchester City, Kevin De Bruyne mai karbar £385,000 a mako.

Asali: Legit.ng

Online view pixel