Likitoci sun fede wani mutum, sun ciro Nokia 3310 da ya hadiye

Likitoci sun fede wani mutum, sun ciro Nokia 3310 da ya hadiye

  • Likitoci a Kosovo sun fede wani mutum bayan ya hadiye Nokia 3310 sukutun guda a cikin sa
  • Bayan mutumin mai shekaru 33 ya hadiye wayar, ya gane cewa rayuwar sa ta na cikin hatsari
  • Da kan shi ya garzaya har asibiti bayan ya ji bakar azaba don likitoci su kai masa dauki

Kosovo - Wani mutum ya hadiye gaba daya waya kirar Nokia 3310 har sai da likitocin da ke Kosovo suka fede shi kafin suka samu nasarar cire wayar.

Kamar yadda shafin Linda Ikeji ya wallafa, mutumin mai shekaru 33 ya hadiye wayar sai dai ta yi wa hanjin sa girma balle ta narke a cikin sa kuma idan batirin wayar ya rube zai iya kone masa kayan ciki.

Kara karanta wannan

Mahaifi ya ƙwace ƴar shi bayan ta haifa ƴaƴa 5 saboda miji ya ƙi biyan sadaki

Likitoci sun fede wani mutum, sun ciro Nokia 3310 da ya hadiye
Likitoci sun ciro wa wani bawan Allah waya kirar Nokia 3310 da ya hadiye. Hoto daga Skender Teljaku
Asali: Facebook

Kamar yadda shafin Linda Ikeji ya ruwaito, Skender Teljaku shi ne babban likitan da ya jagoranci aikin da aka yi wa mutumin kuma ya wallafa hotuna a shafin sa na Facebook.

Ya wallafa hotunan wayar bayan an cire ta da kuma hotunan wayar a lokacin tana cikin sa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Likitan ya samu nasarar cire wayar amma sai da ya raba ta gida uku cikin dabara.

“Ba a samu wata matsala ba,” a cewar likitan.

Kamar yadda Linda Ikeji ta ruwaito, shi da kan shi ya nufi asibiti bayan ya ji radadin azaba bayan hadiye wayar.

Abin Da Yasa Ba Za a Dena Yin Smogul Ɗin Man Fetur Ba, Shugaban NNPC, Mele Kyari

A wani labari na daban, shugaban kamfanin matatan man fetur na Nigeria, NNPC, ya ce kamfanin da wasu hukumomin tarayya za su cigaba da fama da kallubalen fasakwabrin kayayyakin man fetur saboda babancin farashin man fetur a Nigeria da kasashen da ke makwabtaka da ita, rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Barayi sun mayar da kuɗaɗen da suka sata bayan an kai su gaban ƙasurgumin boka

The Punch ta ruwaito Shugaban NNPC, Mele Kyari, ne ya sanar da hakan yayin wani jawabi da ya yi wurin taron tattaunawa da kwamitin Majalisar Dattijai na tsara yadda ake kashe kudade ta shirya.

A cewar wata sanarwa da shugaban sashin hulda da jama'a na NNPC, Garba-Deen Muhammad ya fitar, Kyari ya ce akwai banbancin kimanin N100 a farashin kowanne lita daya tsakanin yadda ake sayarwa a Nigeria da kasashen da ke kewaye da ita hakan yasa yana da wuya hana fasakwabri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel