Mahamady Doumbouya: Waye zakakurin sojan da ya jagoranci juyin mulki a Guinea?

Mahamady Doumbouya: Waye zakakurin sojan da ya jagoranci juyin mulki a Guinea?

  • Kanal Mahamady Doumbouya ne sojan da ya jagoranci juyin mulkin Guinea Conakry kuma kwamanda ne na runduna ta musamman da ake kira GFS
  • Duk da dai babu wasu cikakkun bayanai dangane da farkon rayuwar Doumbouya, amma asalin sa dan kabilar Malinke ne, yankin Kankan da ke gabashin Guinea
  • An samu rahotanni a kan yadda ya halarci makarantar horar da dabarun yaki a birnin Paris da ke kasar Farabsa sannan ya kwashe shekaru 15 cikin kwarewa a aikin soja

Guinea - Kanal Mahamady Doumbouya ne sojan da ya jagoranci juyin mulki a kasar Guinea kuma dama kwamandan runduna ta musamman ta GFS ne a kasar.

Kamar yadda BBC Hausa ta wallafa, a takaice labarin nan zai bayyana tarihinsa da kuma irin horon da ya samu a kasashe daban-daban.

Kara karanta wannan

Atiku: Ya kamata a kirkiri rundunar 'yan sandan da aikinta shine gadin makarantu

Mamady Doumbouya: Waye zakakurin sojan da ya jagoranci juyin mulki a Guinea?
Mamady Doumbouya shi ne gwarzon sojan da ya jagoranci juyin mulki a kasar Guinea. Hoto daga BBC Hausa
Asali: Facebook

Kwararreen soja ne wanda ya samu horo

Kanal Doumbouya kamar yadda rahotanni suka tabbatar, ya samu horon soji mai yawa a kasar Faransa, kuma shi ne jagoran tawagar juyin mulki da ake wa lakabi da National Rally and Development Committee (CNRD).

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ba a samu wasu bayanai masu yawa dangane da farkon rayuwar Doumbouya ba, amma dai an samu bayanai a kan asalin kabilarsa ta Malinke, yankin Kankan da ke gabashin Guinea.

Ya zauna a Forecariah da ke yammacin Guinea inda ya yi aiki a karkashin ofishin kula da yankuna na DST da kuma ayyukan leken asiri.

Ya halarci kwalejin horar da dabarun yaki a Faransa

An samu bayanai a kan yadda ya halarci kwalejin horar da dabarun yaki da ke Paris a kasar Faransa.

Ya kai shekaru 15 a matsayin kwararren soja don a cikin shekarun nan ya halarci yaki a Afghanistan, Cote d’Ivoire, Djibouti, Jamhuriyar Afrika ta tsakiya, Isra’ila, Cyprus, Biryaniya da Guinea Bissau.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta yi nasarar kwato N1trn na kudin sata, Shugabannin APC

Kanal din gwarzo ne na hakika, don ya halarci duk ayyukan nan cikin kwarewa da nasara mai tarin yawa, BBC Hausa ta wallafa.

Ya halarci kwalejojin horar da dabarun yaki a zamanaa na Isra’ila da Senegal, kuma ya samu shaidojin lakantar siddabarun yaki da harkar tsaro.

Ya yi aiki a matsayin wailin dakarun sojin Guinea a Faransa zuwa 2018 lokacin da shugaba Conde ya bukaci ya koma gida don jagorantar gagarumar rundunar GFS wacce ya kafa a shekarar da ta wuce.

Kano: Hukumar yaƙi da rashawa tana shirin karya farashin kayan abinci

A wani labari na daban, hukumar karbar korafin jama’a da yaki da rashawa ta jihar Kano, PCACC, ta bayyana shirin ta na karya farashin kayan abinci a fadin jihar.

Daily Trust ta ruwaito cewa, shugaban hukumar, Mahmoud Balarabe ya bayyana wa manema labarai hakan a ranar Alhamis.

A cewarsa:

“Hukumar ta damu da yadda kayan abinci suka tashi a hannun ‘yan kasuwa wanda hakan ya na wahalar da talakawan jihar.”

Kara karanta wannan

Buhari: Sai bayan na sauka 'yan Najeriya za su gane irin gatan da na yi musu

Asali: Legit.ng

Online view pixel