Gwamnatin Buhari ta yi nasarar kwato N1trn na kudin sata, Shugabannin APC

Gwamnatin Buhari ta yi nasarar kwato N1trn na kudin sata, Shugabannin APC

  • Tun bayan hawan shugaban kasa Muhammadu Buhari mulkin Najeriya a 2015 yana ta gano makudan kudade sakamakon bincike
  • Daga 2015 zuwa yanzu EFCC da ICPC sun gano kudaden da suka kusa naira tiriliyan daya a ciki da wajen Najeriya wanda aka sata
  • Ana amfani da kudaden ne wurin ci gaba da ayyukan bunkasa kasa, cikasa kasafin kudin ayyuka da sauran ayyukan ci gaba

Shugabannin jam'iyya mai mulki ta APC, sun ce kusan makuden kudi da suka kai tiriliyan daya da kadarori shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kwato daga mahandama bayan hawansa kujerarsa a APC, Daily Trust ta wallafa.

A wata takarda da aka fitar a ranar Alhamis, tsohon sakataren hulda da jama'a na jam'iyyar, Lanre Issa-Onilu, mamba na kwamitin rikon kwarya, Barista Isma'il Ahmed, hadimin shugaban kasa, Tolu Ogunlesi da darakta janar na zauren gwamnonin jam'iyyar, Salihu Lukman, sun ce an samu manyan nasarori.

Kara karanta wannan

Buhari: Sai bayan na sauka 'yan Najeriya za su gane irin gatan da na yi musu

Gwamnatin Buhari ta yi nasarar kwato N1trn na kudin sata, Shugabannin APC
Shugabannin APC sun ce gwamnati Buhar ta yi kwace N1trn na kudin sata. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Kamar yadda takardar ta shaida, gwamnati ta na amfani da kudaden da ta gano ne wurin ayyuka na musamman da kuma sanya hannun jari ko kuma a shigar da su cikin kasafin ko wacce shekara.

Daily Trust ta ruwaito cewa, mulkin shugaba Muhammadu Buhari ya jajirce wurin ganin an karbi duk wasu haraji da basuka.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Cikin manyan nasarorin da aka samu akwai: Dala miliyan 322 na kudin da Abacha ya wawura ya kai gwamnatin Switzerland; dala miliyan 311 na kudin da Abacha ya mika Bailiwick na Jersey; dala miliyan 100 da EFCC ta amso daga hukumar madatsun ruwa ta Najeriya (NPA), daga kamfanin mai da gas, akwai pan miliyan 4.2 na kudaden satar Ibori daga gwamnatin Ingila, sai naira biliyan 53 daga FMBN, daga dillalan gidaje.

Akwai sauran dala miliyan 43 kudin jami’an tsaro na Ikoyi da kuma naira biliyan 189 daga kasafin da suka karu da sauransu. Akwai kuma kudaden fansho da aka amsa daga kamfanonin inshora na ciki da wajen kasar nan wadanda mallakin PTAD ne.

Kara karanta wannan

Survival Fund: Gwamnati ta raba wa 'yan Najeriya sama da miliyan 1 kudade N56.8bn

Akwai kasafin ICPC tun daga 2015 zuwa 2018 da aka samo naira biliyan 2, sannan akwai ‘yan kwangila 300 da aka tilasta su mayar da kudaden da suka ki yin ayyuka masu kyau ko kuma suka ki yin ayyukan gaba daya.

A shekarar 2021, EFCC da ICPC sun ci gaba da nemo kudade da dukiyoyi daga hannun kamfanoni da mutane wadanda suka kai biliyoyin nairori.

Tun da shugaba Muhammadu Buhari ya hau kujerarsa, ya amso kudaden da suka kai tiriliyan daya kuma an yi ta amfani dasu wurin kasafi da wasu ayyukan kasa.

'Yan banga sun bindige mai garkuwa da mutane yayin da ya je karbar kudin fansa

A wani labari na daban, 'yan sandan jihar Adamawa sun tabbatar da sheke wani mai garkuwa da mutane da 'yan banga suka yi yayin da ya je karbar kudin fansa daga 'yan uwan wacce ya sace, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya yi Allah wadai da hallaka dan Sanata Bala Na'Allah da aka yi

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Sulaiman Nguroje, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a ranar Laraba a Yola, ya ce lamarin ya faru a ranar 26 ga watan Augusta a karamar hukumar Song ta jihar.

"Rundunar 'yan sandan jihar ta samu rahoto daga 'yan sandan Song a ranar 26 ga watan Augusta kan cewa 'yan banga sun sheke wani da ake zargi da garkuwa da mutane yayin karbar kudin fansa," Nguroje ya ce.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel