Kano: Hukumar yaƙi da rashawa tana shirin karya farashin kayan abinci

Kano: Hukumar yaƙi da rashawa tana shirin karya farashin kayan abinci

  • Hukumar yaki da rashawa da korafin jama’a ta jihar Kano, PCACC, tana shirin karya farashin kayan abinci a jihar
  • Shugaban hukumar, Mahmoud Balarabe ne ya sanar da hakan a ranar Alhamis yayin tattaunawa da manema labarai
  • A cewar sa, hukumar ta damu da yadda farashin kayan abinci a wurin ‘yan kasuwa suka tashi talakawa suna wahala

Kano - Hukumar karbar korafin jama’a da yaki da rashawa ta jihar Kano, PCACC, ta bayyana shirin ta na karya farashin kayan abinci a fadin jihar.

Daily Trust ta ruwaito cewa, shugaban hukumar, Mahmoud Balarabe ya bayyana wa manema labarai hakan a ranar Alhamis.

Kano: Hukumar yaki da rashawa tana shirin karya farashin kayan abinci
Sabon shugaban hukumar yaki da rashawa ya sha alwashin daidaita farashin kayan abinci a Kano. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

A cewarsa:

“Hukumar ta damu da yadda kayan abinci suka tashi a hannun ‘yan kasuwa wanda hakan ya na wahalar da talakawan jihar.”

Kara karanta wannan

Usman Baba Alkali: Na zama IGP a lokacin da a ke tsaka da fuskantar jarabawa

Balarabe ya ce hukumar ba za ta tankwashe kafa tana kallon mugayen ‘yan kasuwa suna dora wa jama’a wahala ba, duk da tsananin rayuwar da kasar nan take ciki, Daily Trust ta wallafa hakan.

“Yanzu muna aiki a kan korafin jama’a ne da kuma yaki da rashawa. Muna aikin tare da majalisar jihar Kano don ganin sun sanya doka kuma mun tursasa ‘yan kasuwa sun karya farashin kayan abinci.
“Cikin dokokin akwai ci gaba da bincike a kan karin farashin kayan abinci da ‘yan kasuwa su ke yi a fadin jihar.
“Ganin halin tsananin rayuwar da jama’a suke ciki, sai mu ka ga ya kamata a ce mun sa ‘yan kasuwa sun daidaita farashin kayan abinci,” a cewar sa.

A cewarsa, dole doka ta tankwasa duk wanda ya yi kokarin bijirewa.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke dan bindigan da ya sace daliban Kwalejin Noma na Afaka

“Dole doka ta zama madubin al’umma. Ba za mu zura ido muna ganin mutane suna yin yadda suka ga dama ba,” a cewar sa.

Balarabe ya bayyana shirin su na ganin sun tankwasa tarbiyyar yara ta hanyar samar da salon koya wa yara sana’o’i a makarantu don su girma da neman na kansu a zuciyoyin su.

Masu garkuwa da mutane sun kashe mace mai juna biyu a Zaria

A wani labari na daban, Mai Martaba Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli ya koka kan karuwar harin yan bindiga, yana mai cewa kisar gillar da aka yi wa mace mai juna biyu a Zaria a matsayin abin damuwa.

Daily Trust ta ruwaito cewa sarkin ya ce kasar na cikin wani lokaci mai wahala, yana mai cewa matsalar ba Nigeria kadai ta shafa ba.

Ya ce matsala ce da ta karade kasashen duniya don haka ya zama dole dukkan masu ruwa da tsaki su hada hannu don ganin an yi maganin abin a cewar rahoton na Daily Trust.

Kara karanta wannan

Sojojin sama sun yi luguden wuta, sun kashe ‘Yan bindiga rututu da su ka fake a jejin Zamfara

Asali: Legit.ng

Online view pixel