Atiku: Ya kamata a kirkiri rundunar 'yan sandan da aikinta shine gadin makarantu

Atiku: Ya kamata a kirkiri rundunar 'yan sandan da aikinta shine gadin makarantu

  • Biyo bayan sace daliban wata makarantar sakandare a Zamfara, Atiku Abubakar ya yi martani
  • Ya bayyana cewa, ya kamata gwamnati ta samar da runduna ta musamman don kare makarantu
  • Ya kuma bayyana kokensa kan yawaitar sace dalibai a yankunan Arewa maso yammacin Najeriya

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya ba da shawarar kirkiro da sabuwar rundunar 'yan sanda don kare makarantu daga hare-haren 'yan bindiga a yankunan da lamarin tsaro yake kara ta'azzara.

Ya fadi hakan ne yayin da yake mayar da martani kan sace dalibai 73 da aka yi kwanan nan a Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Kaya dake Karamar Hukumar Maradun a Jihar Zamfara.

Tsohon dan takarar shugaban kasan na jam'iyyar PDP ya kuma koka kan harin da sace daliban.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari: Zan yi maganin masu ta da hankali da kashe-kashe a Jos

Atiku: Ya kamata a kirkiri rundunar 'yan sandan da aikinta shine gadin makarantu
Atiku Abubakar | Hoto: leadership.ng
Asali: Facebook

A wani rubutu da ya yi a shafinsa na Facebook, Atiku ya bayyana cewa:

“Ina bakin ciki da rahotannin sake sace dalibai a Zamfara. Ga yankin da ke tasowa a fagen ilimi mai mahimmanci, ci gaba da kai hari kan ci gaban mu ba abin yarda bane.
“Watakila lokaci ya yi da za a kirkiri Sashin Jira da Kare Makarantu na musamman don kare makarantu a yankunan da ke fuskantar wadannan hare-hare.
"Idan ba mu dauki matakan riga-kafi ba, ina tsoron cewa ilimi a yankunan da suke dama a lalace na iya fuskantar asarar da ba za a iya gyara ta ba.
"A halin yanzu, ina fatan ana duk wani kokari da za a yi don ganin an dawo da daliban cikin hanzari."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Zamfara ta ba da umarnin rufe kasuwanni da tashoshin man fetur, ta bayyana dalili

An sace dalibai da dama a jihar Zamfara

A baya Legit.ng Hausa ta ruwaito cewa, wasu 'yan bindiga sun sace daliban Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Kaya dake Karamar Hukumar Maradun a Jihar Zamfara guda 73, lamarin da ya girgiza mutane da yawa.

Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da faruwar haka, yayin da ta ce tana ci gaba da bincike kan lamarin, kana ita ta bayyana adadin daliban da aka sace, inji rahoton TVC.

Yankunan Arewa maso yammacin Najeriya na ci gaba da fuskantar kalubalen tsaro, musamman yadda 'yan bindiga ke sace dalibai domin karbar kudin fansa.

Tubabbun 'yan bindiga sun koma ruwa, sun shiga hannun 'yan sanda a Katsina

A wani labarin, Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina a ranar Laraba 1 ga watan Satumba ta gabatar da mutane 12 da ake zargi ciki har da tubabbun 'yan bindiga guda uku bisa laifuka daban-daban da suka hada da fashi, satar shanu da garkuwa da mutane.

Kara karanta wannan

Rufe Makarantun Kaduna: Iyayen Ɗalibai Sun Ce Sun Fara Tura Ƴaƴansu Koyon Ɗinki Da Walda

Tubabbun 'yan bindigan su ne Abdullahi Mai-Rafi mai shekaru 43; Abbas Haruna mai shekaru 34; da Usman Hassan mai shekaru 50, jaridar Punch ta ruwaito.

Kakakin rundunar, SP Gambo Isah, ya shaida wa manema labarai a hedikwatar ‘yan sanda da ke Katsina, cewa ana zargin mutanen uku sun kai hari kan wani makiyayi, Alhaji Gide Suleiman, a ranar 11 ga Agusta, 2021, a dajin Dammarke a karamar hukumar Ingawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel