Wasu ‘Ya ‘yan APC 3, 600 sun kai Mala Buni kotu, suna so a tunbuke shi
- ‘Yan kungiyar SWAGA sun shigar da karar Mala Buni, INEC da wasu a kotu
- Masu goyon bayan Bola Tinubu a zaben 2023 suna so a cire shugabannin riko
- SWAGA tana so ayi watsi da duk zabukan da jam’iyyar APC ta shirya a Ekiti
‘Ya ‘yan jam’iyyar APC na reshen jihar Ekiti da ke tare da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu sun roki kotu ta sauke Mai Mala Buni daga kujerar da yake kai.
Jaridar Punch tace ‘ya ‘yan jam’iyyar suna so kotu ta tsige gwamnan Yobe, Mai Mala Buni daga mukamin na sa na shugaban rikon kwarya na kasa.
‘Yan kungiyar South West Agenda for Asiwaju 2023 da ke cikin APC suna so Alkali ya sauke shugaban APC, sannan ya rusa matakan da ya dauka.
South West Agenda for Asiwaju 2023 mai goyon bayan Tinubu ya zama shugaban kasa tana so a soke zaben duk mazabun da aka yi a watan Yuli a Ekiti.
South West Agenda for Asiwaju ta je kotu
‘Yan kungiyar SWAGA mutum 36 sun shigar da kara mai lamba ta FHC/AD/CS/21/2021 a gaban babban kotun tarayya da ke garin Ekiti kan wannan batu.
Wadanda suka shigar da karar sun nemi Alkali ya zartar da cewa sakamakon zaben mazabun da APC ta shirya bai da hurumin zama a tsari da dokar kasa.
Rahoton yace wadannan mutane sun shigar da karar ta hannun lauyoyinsu ne a madadin sauran mutane 3, 650 ‘yan kungiyar SWAGA da ke garin Ekiti.
Barista Ayodeji Odu da wasu lauyoyi suna karar jam’iyyar APC, Mai Mala Buni, shugaban APC na Ekiti, Paul Omotoso, Samuel Abejide da hukumar INEC.
Da dumi-dumi: Kotu ta kori Gwamna Buni a matsayin shugaban riko na APC, ta dakatar da taron karamar hukuma
Lauyan ya na ikirari Mala Buni ba zai iya rike mukamin shugaban rikon kwarya ba saboda sashe na 187 na kundin tsarin mulkin 1999 bai san da kujerar ba.
SWAGA ta bukaci Alkali ya hana shugabannin APC shirya wasu zabuka a Ekiti nan gaba. Sannan a haramta wa INEC aiki da shugabannin da APC ta fitar.
Sakataren kwwamitin shirya zabuka Femi Akindele, ya yi martani, yace za a hukunta wadanda suka shigar da karar jam'iyya a kotu, maimakon ayi sulhu.
Ya ake ciki a PDP?
Kwanaki PDP ta gabatar da wasu bukatu uku da ta ke da su gaban Gwamnan Ribas, Nyesom Wike yayin da aka ji kwamitin sulhun David Mark ya soma aiki.
A daidai wannan lokaci an ji shugabannin PDP sun zauna da Goodluck Jonathan, sun roke shi ka da ya jefar da jam’iyyar, ya nemi ya koma jam'iyyar APC.
Asali: Legit.ng